Connect with us

LABARAI

Babu Maganar Rage ‘Yan Fansho A Jihar Kaduna —Borokon Zazzau

Published

on

Kungiyar masu karbar fansho ta jihar Kaduna, ta bayar da tabbacin cewar babu wani mai karbar fansho da za a cire sunansa daga cikin masu karbar fansho  a fadin jihar  kàduna.

Shugaban kungiyar masu karbar fansho na jihar  Kaduna, Alhaji Abdu Ramadan Kwarbai, ya  bayyana haka ga wakilinmu da ke Zariya.

Alhaji Abdu Ramadan,wanda kuma  shi  ne  Borokan Zazzau ya ci gaba da cewa, tsarin  da gwamnatin jihar  Kaduna ta fito da shi zai shafi wanda ya rasu ne, ba ma su rai ba.

Duk da haka, Borokan ya yi kira ga masu karbar fansho a jihar Kaduna da su tabbatar sun  je bankunan da gwamnati ta ce a je a dangwala hannun, kamar yadda ta ce a cikin  kwana talatin da  za a yi ana tantance masu karbar fansho a sassan jihar Kaduna.

A game da karin kudn fansho da  Shugaban masu karbar fansho a jihar Kaduna wanda ya dade yana kiran gwamnatocin da suka gabata, sai ya ce nan gaba kadan wannan matsala, za ta zama tarihi, kuma, masu karbar fansho za su tabbatar da haka a Nijeriya, ba a jihar Kaduna  kawai ba.

Alhaji Abdu Ramadan Kwarbai, ya kammala da kira ga masu karbar fansho na jihar Kaduna da su ci gaba da yin addu’o’in samun masarar bukatar sabon tsarin fansho, kamar yadda kungiyar masu larbar fansho a Nijeriya take bukata.

 

Advertisement

labarai