Babu Maganar Sak, Sai Dai Cancanta A 2019 — BCO

An yi kira ga ‘yan Najeriya da su ci gaba da marawa Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, don ceto kasarnan daga kangin da ta samu kanta na rashin kyakkyawan Shugabanci. Zaman shi Shugaban kasa a 2015 ne ya ceto kasarnan daga halin rushewar tattalin arzikin kasa da yawaitar zubar da jini da ta tsinci kanta. Shugaban kungiyar tallata manufofin Muhammadu Buhari ( Buhari Campaing Organisation), ta kasa reshen Jihar Neja, Alhaji Isah Sidi Rijau, ya bayyana hakan ga manema labarai bayan kammala taron da kungiyar ta yi a Minna a dakin taro na hukumar gyaran dokoki ta kasa.

Alhaji Isah Sidi, ya ci gaba da cewar babu wani dan takarar da ke da kyakkyawan manufa a kasarnan kamar Shugaba Buhari, domin ya karbi mulkin kasarnan a lokacin da ta ke tangal-tangal wanda tattalin arzikinta na gab da durkushewa a lokacin, ya yi kokari wajen dawo da martabar kasar a idon duniya haka kuma ya zama gwarzon Afrika a yaki da rashawa wannan abin a yaba ne.

Don haka a dan lokacin da Jam’iyyar APC ta yi mulki bisa jagorancin Shugaba Muhammadu Buhari, kowa ya ga irin ci gaban da aka samu a kasarnan, idan mun duba maganar tsaro da yaki da rashawa, ya taimaka gaya wajen farfado da kasarnan a halin kuncin da makiya ci gaban kasar suka jefa ta, don haka Buhari Campaing Organisation za ta tashi haikan wajen yekuwa ga al’ummar kasarnan kan sake baiwa Shugaba Muhammadu Buhari, damar rike kasarnan na wasu wa’adin shekaru hudu masu zuwa, domin wadannan muradun da kokarinsa na kau da barayin dukiyar kasa tare da tabbatar da adalci a kasar ba zai samu nasara ba sai mun hada kai mun yi aiki tare.

Ba wani dan siyasa mai neman mukami da zai sake shigar inuwar Buhari don ya cuci kasarnan, lallai ne ba zamu amince da sa ke yin Sak ba a zabuka masu zuwa ba, cancanta za mu yi, kowa halinsa ya kawo shi.

Da yake karin haske, Shugaban kungiyar na yakin Arewa ta tsakiya, Hon. Ubale Marafa Kagara, ya ce, Shugaba Muhammadu Buhari ne kadai zai iya ceto kasarnan daga halin da aka jefa ta shekaru aru-aru wanda addu’o’in da bayin Allah na kwarai suka dinga yi ne ya sa Allah ya ba shi nasara a zaben 2015 da ya gabata saboda kyakkyawar niyyarsa ga kasar.

Zamu tsaya tsayin daka da Shugabannin kungiyar na sauran Jihohi wajen wayar da kan al’umma muhimmancin sa ke baiwa Buhari dama a zango na biyu na Shugabancin kasarnan. Nasarorin da ya samu a kasarnan ba shi ne da su ba, mu ‘yan kasa ke da wannan nasarar domin kowa ya ga inda aka fito, jama’a su kara hakuri barazanar da ke tasowa yanzu Gwamnati na daukar matakan toshe su domin zagon kasa ne ake yi na ganin bai dawo ba, amma da yardar Allah, da goyon bayan al’ummar kasa gwamanti za ta dakile komai.

Taron dai wanda shi ne na farko a Jihar Neja, ya samu halartar Shugaban kungiyar reshen Arewa ta tsakiya, Hon. Ubale Marafa da Shugabancin Jiha bisa jagorancin Hon. Isah Sidi Rijau, sai uwar kungiyar Hajiya Aishatu Galadima Gana wanda sun kuduri aniyar kafa Shugabancin kungiyar a yankunan kananan hukumomi ashirin da biyar da ke Jihar.

 

Exit mobile version