Daga Mustapha Ibrahim,
Alhaji Kabiru Sani Kwangila Yakasai Kano, wanda aka fi sani da SKY ya bayyana cewa babu wani mutum a doron kasa da ya kai darajar Malami, domin malamai su ne aka ce magada Annabawa, kuma Annabawa babu wanda ya kai su a doron kasa, domin su ne suka zo da sako daga Allah na abishi a ji tsoronsa a kadaita shi da kuma dukkanin ibadu kamar Kalmar Shahada, Sallah, Azumi, Zakka, zuwa Hajji ga mai iko, da sauran bayanin sako na hani da mummuna da umarni da kyakkyawa. Wannan shi ne aikin shugaban Annabawa da ma sauran halittu, don haka wannan aiki shi ne da mallamai suke yi na koyar da addini da suran mu’amaloli na rayuwa.
SKY ya bayyana haka ne a lokacin bikin yaye daliban makarantar Darul Hijrah Islamiyya da ke unguwar Technical GRA Nassarwa da ke cikin Karmar Hukumar Nassarwa da ke Kano da kewaye, taron da aka gabatar a ranar Lahadin da ta gabata.
“ Har ila yau ya ce mukamin Gwamna, Sarki da sauran shugabanni na da girma da daraja kasancewar su shugabaninmu amma gwamna da sarki da suransu ba su kai daraja Malami ba, domin in ka yi ibada dai dai ko wata mu’amala ta rikon amana, da tsoran Allah da duk wani abin yabo malami ne ya koya ma wannan ce ta tabbabar da Malamai darajarsu ta fi ta kowa,” a cewar Sky.
Shi ma a Jawabin sa shugaban makarantar ta Darul Hijrah Islamiyya Malam Khidir Lawan Balarabe, ce cewa ya yi wannan sauka ta Alkur’ani da wadannan dalibai suka yi ita ce Sauka ta tara, Kuma an yi walimar sauka dalibai 19 ne, a wannan rana, inda aka yaye mata 11 maza 8. A karshe Malamin ya ya ba wa SKY kan dawainiya da taimako da yake ga wannan makaranta da sauran al’umma da sauran al’mura na addinin Musulunci a ko da yaushe.