Ɗan wasan ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Manchester united, Poul Pogba, ya bayyana cewa babu matsala a ƙungiyar duk da cewa Pogba baya buga wasa a ƙungiyar sakamakon ciwo da ɗan wasan yaji.
Pogba dai yasamu ciwo ne makonni biyu da suka gabata a wasan da ƙungiyar ta buga da ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Basel wadda tazo daga ƙasar Switzerland a wasan cin kofin zakarun turai a filin wasa na Old Trafford.
Sai dai ɗan wasa Matic ya bayyana cewa duk da cewa suna kewar pogba amma hakan baisa sun karaya ba zasu cigaba da buga wasanni batare da rashin ɗan wasan ya nu a ba.
Matic yaƙara da cewa kowanne ɗan wasa a shirye yake da yabada gudun mawa a ƙungiyar idan har an sakashi a wasa wanda hakan ba ƙaramin cigaba bane, sannan yace abin farin cikin shine suna samun ƙwallaye a raga sosai ba kamar shekarar da ta gabata ba.
A ƙarshe yace babban abinda yake gaban yan wasan ƙungiyar shine lashe kowanne wasa wanda hakan shine zaisa acigaba da tsoron ƙungiyar kuma shine zaisa ragowar ƙungiyoyi su gane cewa ƙungiyar Manchester united ya shirya lashe kofi a wannan shekarar.
Manchester united dai za ta buga was anta nag aba da Liɓerpool a filin wasa na Anfield a wasa na gaba a gasar firimiya.