Aminu Mukhtar Dan-Alhaji" />

Babu Rabuwar Kai A Tsakanin `Yan APC A Karamar Hukumar Lere – Abubakar Buba

An bayyana cewa kan yayan jam’iyar APC a yankin karamar hukumar Lere ta jihar Kaduna a hade yake babu wata matsala sabanin yadda wasu ke dauka.

Shugaban karamar hukumar ta Lere, Alhaji Abubakar Buba ne ya ambata haka lokacin da yake zantawa da manema labarai a Kaduna.Ya ce babu shakka yanzu kan magoya bayan jam’iyar a hade yake domin kuwa sun riga sun zama tsintsiya madaurinki daya, sannan kuma za su ci gaba da yin aiki tare domin kai wa ga nasara.
Ya ce yanzu haka matsalar da aka fuskanta tsakanin yayan jam’iyar a baya ta zama tarihi kuma kowa na yin abin da ya dace domin cimma dukkan buri.Don haka ya bukaci dukkan magoya bayan jam’iyar ta APC su ci gaba da zama lafiya da fahimtar juna da nufin ganin jam’iyar ta kai bantenta.
Da ya juya ga batun aikin sabunta rijistar zama dan jam’iyar da ke gudana a halin yanzu kuwa, Alhaji Buba ya nuna gamsuwarsa a bisa yadda aikin ke tafiya.Ya lura cewa aikin zai bai wa jama’a damar shiga cikin ta sannan su kuma wadanda ke ciki za su sami damar sabunta rijistar tasu.Ya ce kasancewar an dan yi shekaru ba a sabunta rijistar ba yana da mahimmanci ga jam’iyar ta sabunta rijistar domin kwalliya ta biya kudin sabulu.
Alhaji Abubakar Buba ya kuma nunar da cewa rijistar za ta sa a sami cikakken kundi na magoya bayan jam’iyar a Najeriya baki daya, sannan ya shawarci jama’ar kasar nan su yi amfani da wannan damar domin kara shiga cikin jam’iyar a bisa laakari da dimbin ayyukan alheri da take aiwatar wa.

Exit mobile version