A daidai lokacin da Sufeto Janar na ‘yan sandan Nijeriya, IGP Mohammed Adamu ke kammala wa’adin aikinsa na dan sanda a ranar Litinin din da ta gabata, fadar shugaban kasar Nijeriya ta ce babu ranar da ta ware domin nadin wanda zai gajeshi a matsayin shugaban ‘yan sandan Nijeriya.
Mai magana da yawun shugaban kasa, Malam Garba Shehu shi ne ya shaida hakan a yayin da ke magana ta cikin wani shiri a gidan talabijin din Channels a jiya Litinin, inda ke nuni da cewa bai da masaniya kan wata sanarwa da ta shafi hakan.
Shehu sai dai kuma ya shaida cewar nadin sabon shugaban ‘yan sandan zai gudana ne bisa cancanta da dacewa ba tare da la’akari da wani banbancin kabila ko ta addini ba.
Ya ce, kawai abu guda shine za a maida hankali wajen zakulo hazikin da zai fi bada himma wajen kare rayuka da dukiyar ‘yan Nijeriya, kana za a yi amfani da tsarin tafiyar da shugabanci na ‘yan sandan Nijeriya wajen fitar da sabon shugaban ‘yan sanda.
“Shugaban kasa zai dawo Abuja a ranar Talata. Zai kasance a kujerar mulki ne a ranar Labara. Don haka ban san yaushe ne zai yi wannan ba.
“Abu guda kawai da zan tabbatar muku shi ne a irin wannan wuraren masu muhimmancin gaske babu wani daga kafa, kawai tsarin ne zai yi amfani da kansa wajen tafiyar da lamura.
“Shugaban kasa zai fi son a samu Insifeto Janar na ‘yan sanda wanda zai tabbatar da ba mu kariya ta dukiyoyinmu da lafiyarmu. Ba kuma kabilanci za a daya dubawa ba, dacewa za a yi amfani da shi da kuma wanda ya cancanta.
“Idan ka himmatu wajen nadin shugabanin hukumomin tsaro daga kowace kabila da suke fadin kasar nan, to kuwa za ka yi Insifeto Janar sama da 250 da kuma yin shugaban soji sama da 205 da kuma shugaban sojin ruwa shi ma sama da 250. Lamarin ba zai tafi hakan ba. Hukumomin tsaro su na da tsarin jagorancinsu da ke tafiyar da su.
“Idan muka ce za mu yi amfani da kabilanci ko addini, za mu yi asara ne kawai. Wannan zancen doka da oda ne, ba batun kabilanci ko asali ake ba. kasar nan ta gama wani batun kabilanci tun 1960s, don meye za mu koma hakan a yanzu?”.
Garba ya shaida cewar za a yi nadin ne bisa dacewa da cancanta kuma bisa tsarin jagoranci da hukumar ‘yan sanda ta tsara gami da neman wanda zai tabbatar da kare rayuka da dukiyar jama’a yadda ya dace daga kowace fanni kuwa ya fito muddin shine ya fi dacewa.