El-Zaharaddeen Umar">
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
Home RIGAR 'YANCI

Babu Sauran Shugabancin PDP Ta Katsina – IPAC

by El-Zaharaddeen Umar
January 5, 2021
in RIGAR 'YANCI
2 min read
IPAC Ta Taya Yakubu Murna Kan Sake Naɗa Shi Shugabancin INEC
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram

Gammayar Jam’iyyun siyasa masu bada shawara akan sha’anin mulki da aka fi sani da IPAC sun bayyana cewa bisa ga hukuncin da wata babar kotu a jihar Katsina ta yi na rushe shugabancin jam’iyyar adawa ta PDP to babu sauran shugabanci

Shugaban gamayyar kungiyar ne Alhaji Ibrahim Tukur Saude ya bayyana haka ga manema labarai a Katsina tare da fadin cewa wannan ita ce matsayarsu game da wannan hukunci da kotu ta yi.
Haka kuma ya bayyana cewa hukuncin da kotu ta yanke to babu wani abu gaba da shi saboda haka ne suke kara bayyana matsayinsu karara cewa dole a bi hukuncin da kuma umarnin da kotu ta bada domin cigaban dimokuradiya a jihar Katsina da kuma kasa baki daya.
Alhaji Ibrahim Saude ya kara da cewa suna goyan bayan hukuncin kotu akan wannan al’amari ba su da ja akan abinda aka yi sai dai idan wadanda aka rushe sun daukaka kara wannan wani abu ne na daban.
“muna kira ga uwar jam’iyyar PDP ta kasa da kuma ta jihar Katsina da su gaggauta nada shuwagabanin riko da za su cigaba da tafiyar ragamar jam’iyyar wanda ta haka ne za su samun wakilci a cikin wannan kungiya IPAC” inji shi
Shugaban kungiyar IPAc yana mai cewa PDP su dauki kaddara daga wannan hukuncin da wasu daga cikin ‘ya ‘yan jam’iyyar suka shigar a gaban wata kotu tunda suma suna kai kara kuma suna samun nasara, saboda haka yana ganin wannan ya zama darasi ga ‘yan baya.
A cewarsa wannan al’amari na darbarwar jam’iyyar PDP a jihar Katsina yana neman kawo cikin da tafiyar hawainiya tare da maida hannun agogo baya akan sha’anin siyasa a kasa da kuma jihar Katsina baki daya.
Haka kuma ya bada wata muhimmiyar sanarwa ga sauran ‘yan siyasa da cewa babu sauran shugabacin a jam’iyyar PDP a matakin jiha biyo bayan hukuncin da wata babar kotu ta bayar.
Sannan ya kara da cewa babu wani mutun kowanene da yake da hurumin da zai yi wani abu da ya shafi shugabancin jam’iyyar har sai abinda babar kuto ta bayar idan an daukaka kara nan gaba.
Daga ya ce suna koto ra ga jami’an tsaro da su yi ram da duk wanda ya kara bayyana kansa a matsayin shugaban jam’iyyar PDP a jihar Katsina tare da kara yin kira ga uwar Jma’iyyar PDP ta gaggauta nada sabbin shuwagabanin jam’iyyar matsayin jihar Katsina

samndaads

 

SendShareTweetShare
Previous Post

Ganduje Ya Bukaci Karin Mutum 88,000 Domin Amfana Da Tallafin GEEP A Jihar Kano

Next Post

NAF Ta Dukufa Wajen Fatattakar Boko Haram A Borno

RelatedPosts

IPOB

IPOB Ta Bayyana Dalilin Arangamarta Da Sojoji

by El-Zaharaddeen Umar
1 hour ago
0

A jiya ne 'Yan asalin Biafra (IPOB) da aka haramta...

NDLEA Ta Damke Mutum 544 Bisa Zargin Fataucin Kwayoyi A Borno

NDLEA Ta Damke Mutum 544 Bisa Zargin Fataucin Kwayoyi A Borno

by El-Zaharaddeen Umar
1 hour ago
0

Shugaban hukumar yaki da sha tare da fataucin miyagun kwayoyi...

‘Yan Sanda Sun Ceto Yara Takwas, Sun Kama Masu Juna-biyu A Anambara

‘Yan Sanda Sun Ceto Yara Takwas, Sun Kama Masu Juna-biyu A Anambara

by El-Zaharaddeen Umar
1 hour ago
0

An kama wasu mata takwas, ciki har da mata masu...

Next Post
Rundunar Sojin Sama

NAF Ta Dukufa Wajen Fatattakar Boko Haram A Borno

Domin sanya talla ko karin bayani a tuntube wannan numbar +2348126152609.

ADVERTISEMENT
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us

© 2020 Leadership Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2020 Leadership Group .

Go to mobile version