Ministan Kudi kuma Ministan Tattalin Arziki, Wale Edun ya fayyace cewa ba za a fara aiwatar da cire harajin man fetur na kashi 5 cikin 100 nan take ba. Ministan ya bayyana hakan ne a ranar Talata a wani taron manema labarai a ofishinsa da ke Abuja.
Ministan ya kuma ce ba za a fara aiwatar da harajin man fetur a watan Janairun 2026 ba lokacin da za a fara aiwatar da wasu harajin da shugaba Bola Tinubu ya sanya wa hannu a bana.
- Xi Ya Aike Da Martanin Wasika Ga Wakilan Malamai Na Musamman Don Karfafa Musu Gwiwa
- Sin Ta Gabatar Da Sabon Injin Aiki A Manyan Na’urori Mai Amfani Da Iskar Gas Kirar Gida
“Har yau, babu wani shiri na gaggawa na aiwatar da fara cire harajin kashi 5 na man fetur din da ‘yan kasa suka sha,” in ji Ministan a martanin da ya mayar dangane da cece-ku-ce da jama’a suka yi wa dokar man fetur wanda Ministan ya ce ba sabon abu ba ne sai dai kawai an ɗan yi mata kwaskwarima ne don ta yi daidai da tsarin gyaran haraji da gwamnatin tarayya ke yi.
Ya yi nuni da cewa, dokar za ta bukaci umarnin fara aiki daga ministan kudi kamun a fara.
Edun ya ce, dole ne gwamnati ta zauna tare da masu ruwa da tsaki domin wayar da kan jama’a kafin aiwatar da wannan sabuwar dokar harajin.