A ranar Talata Kamfanin mai na Kasa (NNPC) ta bayyana cewa, babu wani shirin na kara farashin mai kamar yadda mutane suke hasashe. Babban jami’in hudda da jama’a na kamfanin, Dakta Kennie Obateru shi ya karyata wannan jita-jita da ake yi na kara farashin mai a Nijeriya.
Ya ce, “kamfanin NNPC ba ta kara farashin mai a wurin sari ba. Ina mai tabbatar da muku da cewa kamfanin NNPC ba za ta kara farashin mai a wurin sari ba a cikin watan Febrairunn wannan shekarar.”
A cewarsa, kamfanin NNPC ta tanadi mai wanda za a iya amfani da shi a cikin kasar nan na sama da kwanaki 40. Domin haka, mutane su daina jin tsoran a kan cewa mai zai yi karanci. Obateru ya bukaci sashin albarkatun mai na kasa da ta saukar wa ‘yan kasuwa man mara.
“Muna isasshen mai da zai kai sama da kwanaki 40. Idan mutane suka kara farashin mai, rashin albarkatun mai ta kasa za ta dauki mataki a kan hakan,” in ji shi.
Ita ma kungiyar manyan ‘yan kasuwan mai a Nijeriya (MOMAN) ta musanta kara fara shin mai. Ta yi mamayin yadda ‘yan kasuwan mai suke samun wasu bayanan ba daga kamfanin NNPC ba.
Shugaban kungiyar MOMAN, Tunji Oyebanji ya bayyana cewa, babu wani mamba daga cikin kungiyarsa da ya samu wannan bayanin daga wajen kamfanin NNPC. Ya bayyana cewa, gwamnatin tarayya tana ikirarin ta gyara fannin mai, amma har yau ba a bai wa ‘yan kasuwa damar sayar da mai a kan yadda aka kayyade farashin man ba. Oyebanji ya ce, gwamnatin tarayya tana bukatar gyara fannin mai, amma kuma ba ta dauko hanyar da ya kamata ta bi ba. Ya bayyana cewa, gwamnatin tarayya ta tattauna da kungiyar kwadugo a kan hanyoyin da za a bi wajen dakatar da karin mai a Nijeriya.
Masu sayar mai sun tsorata yadda ake sayan mai a wasu jihohi da ke fadin kasar nan, sakamakon karancin man fetur a cikin garin Legas. Mafi yawancin gidajen mai sun kara farashin daga naira 162.50 zuka naira 165 ga kowani litar mai, yayin da wasu har ma sun kai farashin zuwa naira 170.00 a kan kowani lita. Amma wasu gidajen man suka sayarwa yadda farashin ya kamata ya kasance.
A garin Ado Ekiti babban birnin Jihar Ekiti an samu cinkoso wajen sayar da man a jiya. A gidan man First Blessing filling da ke kusa da makarantar kimiyya da fasaha a Ado Ekiti ana sayar da man ne a kan naira 175 a kan kowani litar mai, yayain da gidan man kamfanin NNPC ana sayar da man ne kan naira 165 ga kowacce lita.
A garin Abuja, har yanzu ana sayar da mai a kan naira 162 zuwa naira 162.50, wanda hana daga cikin farashin da gwamnatin ta kayyade wanda ya yi dai-dai da gangan dayan mai a kan dala 43 ga kowace gangan danyan mai.
Maigandi ya ce, an samu farashin mabambamta wanda ‘yan kasuwa suke bukatar gwamnati ta bayar da tallafi.
“Ya kamata gwamnatin tarayya ta dawo da tallafin mai wanda kasuwan man ke takaita ga kan naira 180 ga kowacce lita daya,” in ji shi.