Connect with us

MANYAN LABARAI

Babu Tabbacin Samun Karin Albashi A Watan Satumba

Published

on

Rashin tabbas ya dabaibaye batun Karin mafi karancin albashin ma’aikatan Nijeriya, a yayin da kwamitin masu ruwa da tsaki suka mika rahoton su a yau, dadin dadawa ko za a kara albashin toh lallai ana ganin ba zai yiwu a cikin wannan watan na Satumba ba.

A kwanakin baya ne gwamnatin tarayya ta yi alkawarin kara albashin daga wannan watan na Satumban 2018, mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo ne ya sanar da haka a bikin ranar ma’aikata ta duniya wacce a ke gudanarwa a duk ranar daya ga watan Mayu.

Inda ya nuna lallai batun karin mafi karancin albashi batu ne da ba zai yiwu ayi watsi da shi ba, saboda hakki ne akan gwamnati ta tabbatar da ‘yan kasa da suke yin aiki da guminsu sun samu albashin da ya dace da aikin da suke yi, karin mafi karancin albashin yafi kama da adalci da daidaito.

Shi kuwa shugaban kungiyar kwadago, mista Ayuba Wabba, ya bayyana wa taron kungiyar kwadago ta duniya da aka gabatar a Geneva, cewa dole gwamnati ta tabbatar ta aiwatar da karin mafi karancin albashin a cikin wannan watan na Satumba kamar dai yadda ta yi wa ma’aikata alkawari.

Ma’aikata da dama suna fatan wannan alkawari da gwamnati ta masu, ta tabbatar da shi a cikin wannan watan na Satumba, saboda a cewar su karin da taimaka musu matuka wajen gudanar da rayuwarsu da ta iyalinsu cikin walwala.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: