Umar A Hunkuyi" />

Babu Wanda Ya Isa Ya Tsige Saraki -Dino Melaye

Sanata Dino Melaye, ya kwatanta kiran da ‘yan majalisun Dattawa na jam’iyyar APC ke yi na cewa sai Saraki ya sauka daga shugabancin majalisar a matsayin tatsuniya ce.

Melaye ya fadi hakan ne sa’ailin da yake magana da manema labarai a Abuja, a karshen makon nan, inda yake mayar wa da Sanata Abu Ibrahim, martani kan cewar da ya yi, majalisar ba za ta taba zaunawa lafiya ba, matukar Saraki din bai sauka ba.

Dino Melaye, ya shawarci dukkanin masu tsungular Sarakin da su shafa masa lafiya, ba wai maganan ko a wace jam’iyya ce yake ba, ya kuma tuna masu da cewa, ai ‘yan jam’iyyar PDP su ne suka fi zaban sa a mukamin shugabancin majalisar tun can da farko.

Melaye, ya ce, Saraki, Sanata Ike Ekweremadu, da Yakubu Dogara, duk an zabe su ne a bisa sharadin tsarin mulki ba na jam’iyya ba.

Ya tabbatar da cewa, Sanatocin Jam’iyyar PDP za su yi amfani da karfin su na halaliya, domin kare shugabannin majalisan dattawan biyu da kuma tsarin dimokuradiyya.

Ya ce, duk masoyin dimokuradiyya ba za ka ji yana irin wannan kiran ba, ya ce, PDP wacce ita ce babbar jam’iyyar hamayya a kasar nan za ta ci gaba da kare tsarin na dimokuradiyya.

“Tarihi zai sajjala duk rawar da kowa ya taka a kasar nan. Kafin mutane su fara tserewa daga jam’iyyar ta APC, sau nawa ne ‘yan majalisun na APC suka ziyarci fadar ta shugaban kasa.

“Duk wani yunkuri na a tsige Saraki zai zama tatsuniya ne. kamata ya yi mu fuskanci abin da zai ciyar da kasarmu gaba, sai dai ba na mamaki, masu wadannan maganganun daman ba masu bin dokokin kasa ne ba, da tsarin mulki, dokokin majalisar ta dattawa da abin da ya dace.

Kan ko wace Jam’iyya ce ke da rinjaye yanzun a majalisar, Dino Melaye ya ce, in majalisar ta dawo hutu kowa zai ganin ma idon sa.

Exit mobile version