Kamfanin sufurin Jiragen sama na Air Peace ya ce babu wani Jirginsa da aka kwace a Atlanta ta kasar Amurka.
Kamfanin ya ce ba shi da wata alaka da wani Jirgin sama da aka ce na wani dan Nijeriya ne wanda hukumomi a kasar Amurka suka kwace a bisa cuwa-cuwar kudi.
A cewar shugaban sashen yada labarai na kamfanin na Air Peace, Mista Stanley Olisa, kamfanin ba ma shi da wani Jirgi a yanzun haka a kasar ta Amurka.
Ya ce: “Alakanta kamfanin na su da Jirgin da aka kwacen a kasar ta Amurka, aiki ne na masu son kawo wa kamfanin cikas a nan cikin gida, wadanda suka dukufa domin ganin sun durkusar da kamfanin na Air Peace da kuma mamallakin sa.
“Tuni mun sami labarin cewa ainihin mamallakin Jirgin tuni ya bayyana a kotu a ranar Talata, a kasar ta Amurka, amma abin takaici har yanzun wasu mutane suna kokarin alakanta Jirgin da kamfanin na Air Peace.