Babu Wanda Ya Tilasta Ni Na Shiga Jam’iyyar APC — Matawalle  

Matawalle

Daga Yusuf Shuaibu,

Gwamnan Jihar Zamfara, Bello Matawalle ya bayyana cewa ya sauya sheka zuwa jam’iyyar APC domin ya karfafa hadin kan siyasa a cikin jiharsa. Mashawarcin gwamnan ta fannin yada labara, Yusuf Idris shi ya bayyana haka, sannan ya musanta rahoton da ake yayatawa a kafafen yada labarai cewa an tilasta wa gwamnan ne shi ya sa ya shiga cikin jam’iyyar APC domin ya samu damar dakatar da kashe-kashe a cikin jiharsa.

 

“An san cewa Gwamna Matawalle yana daya daga cikin shugabannin kasar nan da suke fadin magana sannan su cika, ya sauya sheka zuwa jam’iyyar APC ne saboda ya karfafa siyasar hadin kai a jiharsa domin ya kara karo ci gaba ga mutanensa,” in ji Mista Idris.

Kakakin Gwamnan ya kara da cewa gwamnan ya sauya sheka ne sakamakon goyan bayan da yake samu a wajen shugaban kasa Muhammdu Buhari da jam’iyyar APC a kan dukkan al’amura da suka shafi jiharsa.”

Mista Idris ya bayyana cewa shugaba Buhari da gwamnonin jam’iyyar APC sun yi kokari wajen tallafa wa mutanen jihar, wanda suka kara wa gwamnan gwarin gwiwa wajen gudanar da shugabanci nagari.

 

“Babban burin da ya sa gwamnan ya shiga cikin jam’iyyar APC shi ne ya kara aiki tukuru wajen gudanar da kyakkyawan shugabanci, amma gwamna Matawalle bai shiga jam’iyyar APC ba saboda samar da tsaro kamar yadda ake yayatawa a wasu kakafen yada labarai na kasar nan,” in ji shi.

 

Gwamna Matawalle ya dai sauya sheka daga Jam’iyyar PDP zuwa APC ne a makonnin da suka gabata. Ya shiga cikin jam’iyyar mai mulki ne tare da dukkan ‘yan majalisar tarayya da na jiha a Zamfara, amma sai dai mataimakinsa, Mahdi Aliyu Gusau  da wani dan majalisar jiha mai suna Kabiru Yahaya sun yanke shawarar suna nan a jam’iyyar PDP.

Exit mobile version