Connect with us

DAGA BIRNIN SIN

Babu Wani Al’amari Da Zai Iya Bata Huldar Abokantaka Dake Tsakanin Sin Da Afirka

Published

on

Hua Chunyin, kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin ta bayyana a Jumma’a a nan Beijing cewa, shaidu sun sha nuna cewa, kasashen Afirka sun ki yarda a haddasa rashin jituwa a tsakaninsu da kasar Sin.

Rahotanni na cewa, a kwanan baya, sakataren harkokin wajen kasar Amurka Mike Pompeo ya ce, kasarsa ta lura da cewa, kasar Sin da kamfanoni masu zaman kansu na kasar sun bai wa kasashen Afirka taimako da bai taka kara ya karya ba. Sin za ta bai wa kasashen Afirka rancen kudi ta hanyar da ba ta dace ba a daidai wannan lokacin da ake fama da annobar COVID-19, hakan wani salo ne na jibgawa kasashen Afirka basussuka da yawa.
Dangane da kalaman Pompeo, madam Hua Chunying ta nuna cewa, “kasar Sin da kasashen Afirka abokai tamkar ’yan uwa wadanda suka taba sha wahala tare. Mr. Moussa Faki Mahammat, shugaban hukumar gudanarwar kungiyar AU ya taba bayyana cewa, Sin da Afirka abokan arziki ne, kuma abokan dake yaki tare, babu wani al’amari da zai iya canja ko bata huldar abokantaka dake tsakaninsu. Lalle, hakikanan matakan da sassan Sin da Afirka suka dauka tare sun shaida cewa, zumuncin dake tsakanin kasashen Sin da Afirka ya ratsa zukatan jama’a, kuma babu wanda zai iya bata shi ko kadan.
Sannan madam Hua ta nuna cewa, a yayin da ake fama da annobar Korona ta COVID-19, kasashen Sin da Afirka sun tallafa wa juna, suna kuma yakar annobar cikin hadin gwiwa. Shugabannin kasashen Afirka fiye da 50 sun aika wa shugabannin kasar Sin sakwanin jaje da tallafi. A bangaren kasar Sin, a cikin sahihanci ta sha samar da dimbin kayayyakin kandagakin annobar, har ma ta tura tawagogin jami’an kiwon lafiya zuwa kasashen Afirka.
Daga karshe dai, Hua ta jaddada cewa, yanzu kasashen Afirka na fuskantar kalubale a fannoni daban daban. Kasar Sin na fatan sassa masu ruwa da tsaki za su mai da hankali kan taimakawa kasashen Afirka wajen yaki da annobar, za su kuma girmama jama’ar Afirka. (Mai Fassarawa: Tasallah Yuan)
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: