Babu Wani Dan Nijeriya Da Ya Kai Ni Kishin Al’umma –Sule Lamido

Dan takarar Shugabancin kasa a inuwar Jam’iyyar PDP, Alhaji Sule Lamido, ya bayyana cewar idan Allah ya kai shi ga zama Shugaban kasar Nijeriya, zai ceto al’ummar kasar ne daga halin yunwa da fatarar da suka tsinci kansu a karkashin mulkin zalunci da danniya irin na Jam’iyyar APC karkashin jagoranci Shugaban kasa Muhammadu Buhari.
Sule Lamido, ya bayyana hakan ne a lokacin da yake gudanar da yakin neman zabensa na tsayawa takarar Shugabancin kasar nan a inuwar Jam’iyyar PDP idan Allah ya kaimu shekarar 2019 mai zuwa, wanda aka yi a Sakatariyar jam’iyyar PDP dake kaduna.
Sule Lamido wanda ya gudanar da jawabin sa a cikin kakkausar murya, ya bayyana wa magoya bayansa cewar, ya yanke shawarar fitowa ce saboda ya nemi kujerar Shugabancin kasar nan, ne domin ya share ma ‘yan Nijeriya hawaye dangane da halin kunci, yunwa, fatara da talauci da suka tsinci kansu, amma ba wai, ya fito domin ya raba kan al’ummar kasar nan ba ne, kamar yadda abubuwan da suke faruwa Gwamnatin APC karkashin jagorancin mulkin Buhari ke yi ba.
Ya kara da bayyana cewar, “ Insha Allah ina son na tabbatar maku da cewar, zan dawo da martabar jam’iyyarmu ta PDP mai albarka kamar yadda kowa ya san ta a da, bayannan kuma zan ceto al’ummar wannan kasa daga halin kuncin da suka tsinci kansu a irin wannan bakin mulkin Ukuba na jam’iyyar APC.”
“Ina mai tabbatar maku da cewar, babu wani Dan Nijeriya wanda ya kai ni kishin al’ummar Nijeriya, da ma ita kanta Nijeriya, domin na tabbata da cewa, duk wannan bita da kullin da ake yi min, ana yi min su ne saboda a dukufar min da irin kwarjini da soyayyar dake tsakani na da ‘yan Nijeriya, wadanda suka amince dani, suka yarda da irin manufofina, wadanda suka yarda da cewa, tabbas idan har Allah ya kaini ga gaci, ‘yan Nijeriya zasu yarda da cewa sun sami shugaba mai kishinsu, mai kishin kukansu, ba irin wannan shugaban da yake kan mulki ba yanzu.”
Sule Lamido ya kara da cewar, “ ‘yan jam’iyyar APC masu cewa mu barayi ne, wai mun sace dukiyar kasar nan, wannan ba gaskiya ba ne, domin babu manyan manyan barayi, wanda suka wuce irin ‘ya’yan jam’iyyar APC, saboda kowa ya shaida yadda yawancinsu suka sace dukiyar kasar nan, suka gudu suka koma jam’iyyar a APC domin neman mafuka, amma ba domin kishin ‘yan Nijeriya ba.”
“Kuma ina so na kara tabbatar ma da ‘yan Nijeriya , matukar wannan gwamnati ta ‘yan zalunci basu kawo karshen kashe kashen da ake yi a wannan yanki namu na Arewa ba, irin su Zamfara, Birnin Gwari, Sokoto, Filato da dai sauran su, to ya zama wajibi ga wannan Shugaban kasar da ya sauka daga kan shugabancin kasar tun kamin lokacin zabe yazo, domin ya nuna ma duniya irin gajiyawarsa karara, domin kuwa ai dama mun dade muna fadin cewa, mun fi kowa sanin wanene Buhari, mun san ba zai iya rike mulkin kasar nan ba.”

Exit mobile version