Mustapha Abdullahi">

Babu Yadda Za A Ce Mace Ta Kashe ’Ya’yanta Tana cikin Hayyacinta –Malam UMar

Malam Umar Hashim Kwanar Mai Shayi, Unguwar Sanusi cikin garin Kaduna, masani ne a game da al’amuran bincike a kan Magunguna da Tarihi, kuma Malamin addinin Islama, sannan mai kishin ganin an samu ingantacciyar al’umma da ke da makarantar Koyar da matasa ilimi.

Cikin wannan tattaunawar, Malamin ya yi bayani kan irin lamarin cututtukan aljannu, sihiri da sauran ire-iren wadannan, inda har ya tabo batun matar dnan a ake ganin ita ta kashe ‘ya’yanta guda biyu a Kano. Ga dai yadda tattaunawar da kadance da Mustapha Abdullahi.

Game da matar da ake ta yayata cewa ta kashe ‘ya’yanta ta hanyar yankasu da wuka a Kano. Shin a bisa mahangar Malamai, yaya abin yake?

Advertisements

Da farko dai za mu ce Inna lillahi wa’inna alaihi raji’un. Hakika ita wannan baiwar Allah abu ne da ya kamata a tausaya mata a kuma a jajanta mata, domin ita ce wadda ta yi nakudar wadannan yaran kuma ita ce ta dauki dawainiyarsu har suka kai wannan shekaru, amma a karshe wadansu abubuwa suka taso. To bisa hakan a kan samu hanya ta sihiri a juyar da kwakwalwa

Domin Allah ta’ala ya fada cewa idan shaidan ya ribaceka, to ka nemi tsari ga Allah, domin lokacin da shaidan ya tisgeka za ka iya aikata abubuwa da yawa. Kuma idan ka fusata sai ka samu ruwa ka yi alwalla saboda fushi ya kan tashi ne daga garwashin wuta, kuma shaidan ya kan ingiza mutum ya shiga cikin tashin hankali da turka-turka.

Ina tabbata maka, duk dadin da Annabi Adamu ya zauna a cikin Aljannah, ya fita ya bar wannan ni’ima ta dalilin Shaidan, amma daga karshe, Allah ya karbi tubarsa, sannan maganar juyewar kwakwalwa mutum ya rasa halin da yake har ya aiwatar da wani abu da za a ce son me ya yi wannan abu ne ba boyayye ba, domin Allah ya fadi cewa akwai ranar da mace za ta manta da abin da ke cikin cikinta, sannan kuma mai ciki ta haifar da abin da ke cikin cikinta, za ka ga mutane suna maye, amma ba su sha giya ba, a zamanin, ukubar Allah ce ta tsananta.

Saboda haka wannan zai tabbatar maka, wannan zai iya faruwa, idan har ya tabbata Junnu ne, hakan zai iya faruwa a firgita mutum tunaninsa ya zamo ya dauke, wannan kuma ba karya ba ne, domin kur’ani ya tabbatar da hakan. Sannan idan har aka ce sihiri ne, shi ma ba karya ba ne, domin ya faru ga Manzon Allah, wanda ya debi tsawon kwanaki yakan tambayi inda zai kwana daga cikin iyalansa. Don haka wannan zai tabbatar maka a kan iya yi wa mutum wani abu da kwakwalwarsa za ta iya daukewa a kuma yi amfani da tunaninsa ya aikatar da abin da zai yi da-na-sani.

Daga cikin tarihi zai yi wahala ko a cikin tarihin magabata ka ji an ce ga inda mace ta kashe danta, sai dai abin da ya gabata na tarihin magabata, shi ne Larabawa idan aka yi masu haihuwa na ‘ya’ya mata sukan dauke su su je su haka rami su rufe su, amma iyaye mazan ne, ba mata ba, domin mata ba su yarda a dauki ‘ya’yansu, wannan ya taba faruwa a lokacin Bani Isra’ila.

A lokacin daya daga cikin Annabawa, wala Allah ko dai lokacin Annabi Musa ko lokacin Suleiman, wasu ‘yan mata sun tafi za su yi wanka sun ajiye ‘ya’yansu guda biyu a lokacin da suka ajiye ‘ya’yan biyu, Zaki ya zo ya dauke na wadanda suke wanka.

To ashe ya dauki na babbar ne, amma da aka fito daga wurin wanka ita babbar sai ta rike yaron jinjiri ta ce nata ne, ita kuma karamar ta ce ba ta yarda ba, ita ma nata ne, suka yi ja-in-ja, sai gaban Annabi Suleiman, a lokacin da suka je gaban Annabi Suleiman, Alaihissatu wassalam ya tambaye su, kowace ta ce da nata ne Annabi Suleiman ya ce sai dai a dauko wuka domin a yi hukunci. Lokacin da aka dauko wukar sai ya ce to, za a raba dan nan gida biyu, ke ki dauki rabi, ita ta dauki rabi, nan take karamar ta ce in haka ne, ta yafe.

Ba zai faru ba daman a yanka, amma hikima irin ta Annabi Suleiman ya yi masu haka, sai karamar ta ce ta yafe, daga nan sai Annabi Suleiman, ya gane cewa dan ba na babbar ba ne, na diyar ne.

Don haka idan ka duba a lokacin da aka haifi Annabi Musa Alaihissalatu wassalam uwarsa da ake kokarin a kashe ‘ya’ya jira-jirai ita Allah ya taimake ta da daukar dan ta Jefa a cikin Teku domin alkawalin Ubangiji ya yi alkawalin zai dawo mata da shi. Idan mun duba duk yadda ake tunani cewa ita wannan mata za ta iya kashe danta zai yi wahala kamar yadda na gaya maka.

Don haka wannan baiwar Allah, dole ne a tsaya a lura bisa abubuwan da na lissafa maka, akwai sihiri na ture akwai kuma sihiri wanda ake iya hada shi da Aljani ya canza mata siffar ‘ya’ya, dukiya ya kan faru ya fada ga ‘ya’ya ko mutunci da ‘ya’ya. Saboda haka maganar sihiri abu ne mai sauki wanda dan Adam kan iya shiryawa domin ya cutar da wani.

Maganar wannan baiwar Allah ta yanka ‘ya’yanta ko maganar kishi, wannan alal hakika mu da muke gudanar da bincike bisa ga halaye na dan Adam da kuma bincike a kan tarihin magabata ba mu ga haka ba don haka ba tunanin wannan mata ta yanka ‘ya’yanta a tunanin cewa ‘ya;yanta ne ta yanka, wannan hakika akwai abin bincike.

Saboda haka Allah ne kadai zai iya fitar da wannan baiwar Allah ga halin da ta ke ciki, saboda duk wanda ya ke son da bai kai Uwa ba, shi ya sa da yawa Uba ya kan kori dansa, amma uwa zai yi wahala ta kori danta, domin ita kadai ta san wahalar da ta sha, shi ya sa aka ce nakuda daya tana matsayin shahada ga duk matar da ta yi nakuda. Don haka zai yi wahala a ce uwa ta kashe ‘ya’yanta.

Shin Malam, a cikin ayyuka irin na ku na bayar da magani, yana hadawa da mata, shin kun taba samun wani batu mai kamar haka na tsananin kishi, kamar yadda ake ta yadawa, domin wasu na cewa don an yi mata kishiya ne ta dauki mataki irin wannan?

Hakika, mata sukan iya yin wani abu da ya shafi kishi, sukan yi kokari su ga bayan ita kishiyar ko su Jefa mata wata Larura, kuma ma takan iya yin wani abu da ya shafi hushi kamar yadda na fada. Shi kuwa shaidan a lokacin Fushi yake samun dama, kamar yadda na gaya maka, akwai fushi ba, kuma ni ne na fadi ba, Kur’ani ne ya fada cewa daga lokacin da ka samu tusguwa irin ta Shaidan ka nemi tsari.

Shi kuma Manzon Allah ya ce ka nemi ruwa ka sanyaya domin fushi ya kan huru ne kamar garwashi, kuma in ya faru babu abin da ba zai iya faruwa ba akwai kunci shi ne ake cewa Tawatturi. Akwai kuma Irhak, sannan kuma akwai wanda ake kiransa Kalaku, mutum yakan fita daga cikin yanayinsa, akwai kuma Huzna, akwai Gammmu, akwai Hammu dukkansu nau’i ne na bakin ciki.

Akwai Hammu da Gammu su ne ke iya sanyawa mutum ya yi wani abin da bai taba tunani ba, sai daga baya ya yi da-na-sani, amma irin wannan Hammu da Gammu bai kama Ummiyya, wato uwa har ta yi wa ‘ya’yanta, akwai wanda za ta yi misali ta dauko abin duka ta buga, ba ta yi tsammanin cewa ta aikata ba, ta kan dawo ta yi da-na-sani.

Wannan zai ba ka mamaki daga daya aka je ga biyu, hakika mata sukan iya samun kishin da za su Kassara Amarya ko ita Amaryar ta nemi ta Kassara uwargida, kuma muna samun hakan, amma yakan tsaya ga kishin ne. Sannan kuma ana samun wanda za a yi wa miji don a Kassara shi, duka muna samu, ko a zuba Ruwan Zafi a kona shi, ko a zuba Fetur a kunna wuta, ko kuma a yi wani abu da za a sa cikin abinci don a Kassara shi, to wannan duk ana samu.

Ka ga babu wata fa’ida da ake tunanin, wanda don shi aka yi kishi kuma a kashe shi to, me zai bayar da fa’ida ga mutumin da ake kishi don shi kuma an kashe shi? Ka ga ke nan an dai jawo bala’i, akwai abin da za a iya yi, amma mafi yawa wanda ke faruwa irin wannan a tarihance ba mu taba ji ba, a ce Uwa ta kashe ‘ya’yanta. Ko matan da ake cewa suna kashe ‘ya’ya za ka tarar wata ce ta samu ciki, wanda ba na aure ba, wanda wani lokaci Uwarta ce ma za ta kashe, amma ita da ta Haifa zai yi wahala ta kashe da kanta.

Akwai matsaloli da dama da zai nuna cewa wannan baiwar Allah a kara bincike tukuna, kada mutane su fada cikin tarkon da ba za su iya fita ba, Allah ka kare mu.

Shin akwai wata fadakarwa ga magidanta Maza da Mata domin guje wa samun fadawa cikin wata larura irin wannan?

Shi ka’idar aure adalci aka ce ka yi, addinin Islama hakika ya bayyana yadda za a yi zaman aure, har ma a samu rabuwa. Kur’ani cewa ya yi ka zauna da ita da adalci da kyautatawa, kuma ka sake ta kana mai kyautata mata, ba tare da ka musguna mata ba. Da yawa akwai matan da suke yin aure ma ba su isa su yi auren mata biyu ba, suna da abincin da za su ciyar da matan, amma ba su da tarbiyya da kuma hikima na su zauna da matan guda biyu. Saboda haka ire iren irin wadannan su kan rusa tarbiyya, kuma su rusa zaman gidansu.

Sannan da yawa akwai Namijin da ya kan yi aure ne domin kawai a ce yana da mata guda biyu, har ma gasa ake yi a filin tattaunawa, wannan ya ce kai a zamanka mai Mata daya ka kasa kara Mata, wanda kuma ba haka abin yake ba. Kur’ani shi ya rigaya ya ba da zabi, ko biyu ko Uku ko guda hudu, idan kana jin tsoron ba za ka iya yin adalci ba, domin adalci shi ne jagoranci, duk al’ummar da babu adalci a ciki ba za ta iya bayar da abin da ake bukata ba.

Duk Namijin da bai da adalci, to gidansa ba zai tashi da kyau ba, ba zai iya tarbiyyar gidan ba, domin idan aka haihu hakika zai hada ‘ya’yansu su zama masu gaba, domin duk abin da kake gani a cikin gida na tabarbarewar tarbiyya da rashin tarbiyya, ya tattaru ne a kan Mazaje.

Karin auren da ake yi, idan mutum zai yi adalci gidansa zai zauna ba tare da matsala ba, amma daga ranar da ya Sanya rashin adalci ya dauki sirrin wannan ya kai wa waccan, duk abin da suka yi da wancan dakin ya zo ya gaya wa wannan, to hakika akwai matsala. Kuma masu irin wannan bai kamata su hada mata biyu ba, domin su ne ke sanya matansu su tsallake, kuma suna shiga ta hanyar yi masu bokanci wanda daga nan ne ake samun matsaloli da dama domin ta nan ne ake shirya masu yadda za su cutar da abokanan zamansu, yadda ake shirya masu yadda za su cutar da hatta mijin.

A karshe dai abin da nake fada shi ne, abin da Allah ya fadi a cikin littafinsa, in kuna tsoron ba za ku yi adalci ba, ku zauna da mace guda, wannan shi ne hakikanin maganar da ta zo daga sararin sama, daga kuma bakin Allah madaukakin Sarki.

Adalci shi ne jagorancin gida, adalci shi ne jagorancin kamfani, adalci shi ne jagorancin sana’a, adalci shi ne jagorancin wadanda ke karkashinka, kuma adalci shi ne jagorancin al’umma daga sama har kasa, idan babu adalci kamar yadda Allah ya daidaita sama da kasa, idan ba domin adalci ba da sai an samu tusgiro a cikin sama da kasa, Allah sai da ya daidaita su domin adalci.

 

Exit mobile version