Yusuf Shuaibu" />

Babu ’Yar Rufa-rufa A Kasafin Kudin 2021 – Buhari

A ranar Asabar ce, shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya tabbatar wa ‘yan Nijeriya cewa, gwamnatinsa za ta fito da bayanan kudade a fili domin kowa ya gani ba tare da ta more wani abu ba. Haka kuma, ya tabbatar da aiwatar da dukkan kasafin kudin shekarar 2021 a fili domin cimma burikan da aka saka a gaba, yayin da ya yaba wa majalisar kasa bisa gudanar da aiki tukuru wajen amincewa da kasafin.

Da yake zantawa da manema labarai a garin Daura bayan ya kammala sabunta rijista na jam’iyyar APC, shugaban kasa ya bayyana cewa, an tsara kasafin kudi ta yadda zai dace da manufofin gwamnati, za mu yi iya bakin kokarinmu wajen ganin an aiwatar da kasafin kudin yadda ya dace.
A cikin bayanin mashawarcin shugaban kasa ta fanin yada labarai, Garba Shehu ya bayyana cewa, shugaban kasa ya ce, “za mu umurci ma’aikatu da rassa da hukumomin gwamnati da su bi tsarin kasafin kudi yadda ya kamata domin mu sami goyan bayan majalisar kasa a kasafin kudin shekara mai zuwa. Da hakan ne za mu iya yi musu bayanin abin da muka amsa da kuma yadda muka kashe.
“A ko da yaushe a shirye muke mu bayyana wa ‘yan Nijeriya da kuma majalisar kasa. Babu wani abin da zamu boye,” in ji shi.
Shugaban kasa Buhari ya kara da cewa, gwamnatinsa ta fi mayar da hankali a kan noma wajen farfado da tattalin arzikin kasar nan.

Exit mobile version