Babu Yunwa A Nijeriya- Ministan Noma

Ministan noma da ci gaban karkara, wato Sabo Nanono ya bayyana cewa; Nijeriya na noma yawan abincin da take iya ciyar da kanta, sabanin rahotannin da ake yadawa cewa akwai yunwa a kasa.

Nanono ya bayyana hakan ne a wani taro da ya gudana a ranar Litnin a birnin tarayya Abuja. A wani mataki na tunawa da ranar da aka ware a matsayin ranar abinci ta duniya wanda zai gudana a ranar 16 ga watan Oktoba 2019.

Nanono ya kara da cewa; bai kamata a rika yada cewar akwai yunwa a Nijeriya ba, inda ya tabbatar da cewa; akwai dai wuraren da gwamnatin tarayya da kuma masu ruwa da tsaki a harkar noma da ba su kammala cike wa ba.

A cewar Ministan, an ware ranar abinci ta duniya ne domin a tattauna batun  samar da abinci.

 

Exit mobile version