Badaƙala A Hukumar NNPC: Ya Kamata A Yi Wa Tufkar Hanci

Jim kaɗan bayan ɗarewar jam’iyyar APC kan karagar mulkin Nijeriya, gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ta himmatu wajen ganin ta magance cin hanci da rashawa wanda ya daɗe yana ci wa al’ummar ƙasar nan tuwo a ƙwarya.

Da yawan mutane sun gamsu cewar, badaƙalar cin hanci da wawashe dukiyar al’umma a manyan ma’aikatun na kan gaban wajen hana ƙasar motsawa ta fuskar more kayayyakin jin daɗin rayuwa.

A gwamnatin da ta shuɗe, kusan za a iya cewar, an yi badaƙala ta inna-naha da dukiyar jama’a, inda aka mayar da lalitar gwamnati tamkar saniyar tatsa, wanda gwamnati mai ci a yanzu ta yi alƙawarin zaƙulo waɗanda ke da hannu domin hukunta su, sannan kuma ta magance afkuwar hakan a nan gaba.

Kamfanin kula da sha’anin Man Fetur watau NNPC, ya zama wata maɓuɓɓuga da ake fakewa da ita wajen ƙoƙarin yi wa lalitar gwamnati ƙarƙaf. Babu ɗan Nijeriya da zai manta da irin tu’annatin da Ministar Man Fetur, Diezani Alison Maduekwe ta yi ƙarƙashin mulkin Jonathan, wanda zancen da ake yi zaman Nijeriya yana nema ya gagare ta, sakamakon shari’a da take fuskanta a ƙasar Ingila.

Bayan shuɗewar waccan gwamnati, Shugaba Buhari ya naɗa Ibe Emmanuel Kachikwu shugaban kamfanin, kafin daga bisani ya ba shi ƙaramin Ministan Mai, shi kuma ya riƙe babban kujerar ministancin.

Dakta Maikantin Baru, ya samu nasarar zama shugaban kamfanin NNPC sakamakon ƙarin matsayi da Kachikwu ya samu. Sai dai alamu sun bayyana ƙarara, akwai matsala kwance wadda ya kamata tun da wuri a yi wa tufkar hanci.

‘Yan Nijeriya sun yi mamaki matuƙa da ɓullar labarin taƙaddama tsakanin manyan jami’an gwamnatin guda biyu. A wata wasiƙa da ministan ya aika wa Shugaba Muhammadu Buhari, ministan ya zargi shugaban kamfanin da yin ba daidai ba da kuma rashin ɗa’a.

A cikin wasiƙar, wadda kusan dukkanin jaridun Nijeriya suka yi ta buga labarin, ministan ya zargi Shugaban NNPC, Maikanti Baru da ɗaukar manyan ma’aikatan kamfanin da kuma ba da kwagilolin da suka haura dala biliyan 25 ba tare da amincewarsa ba. Saɓanin yadda doka ta tanada, wato sai ya nemi yardar ƙaramin ministan, wanda shi ne shugaban hukumar da ke sa ido kan NNPC.

Hakazalika ministan ya ce, “da na nemi sanin abin da ya sa shugaban NNPC ɗin yin hakan, sai ya gaya min cewa shugaban Buhari ne ya amince da ɗaukar ma’aikatan da kuma ba da kwagilolin.”

Haƙiƙa irin wannan taƙaddama tsakanin maigidan da yaronsa a gwamnatin Buhari, na ci gaba da bawa masana siyasa ciwon kai, duk da dai masu iya magana kan ce, “tsakanin harshe da haƙori ma ana saɓawa” amma lamari a wannan janibin sai ƙara ta’azzara yake.

Kodayake Majalisar Dattawan Nijeriya ta kafa wani kwamitin bincike da zai duba zarge-zargen da ministan ya yi a cikin wasiƙar.

Da take amincewa da ƙudirin da Sanata Samuel Anyanwu mai wakiltar Imo ta Gabas da kuma Sanata Kabiru Marafa mai wakiltar Zamfara ta Tsakiya suka gabatar, majalisar ta kuma ba da umarnin tsawaita binciken zuwa sauran wasu badaƙalolin da aka ce an tafka a wani reshen Kamfanin na NNPC (NNPC Trading Company).

Kwamitin da aka ƙora wa alhakin binciken bisa jagorancin Sanata Aliyu Wamakko, ya kuma ƙunshi mambobi kamar haka: Sanata Taayo Alasoadura, Sanata Kabiru Marafa, Sanata Albert Bassey, Sanata Sam Anyanwu, Sanata Ahmed Ogembe, Sanata Chukwuka Utazi, Sanata Rose Okoh da kuma Sanata Baba Kaka Garbai.

Kamata ya yi binciken da za a yi majalisar ya zama sabon yunƙuri na daidaita tsakanin ministan man, Kachikwu da shugaban kamfanin na NNPC, Maikanti Baru. Ya zama wajibi a kwantarwa da ‘yan Nijeriya hankali, musamman yanzu da tambayoyi suka cika zukatan jama’a kan me yake faruwa a wannan babbar ma’aikata.

Idan muka dubi girman ma’aikata kamar NNPC, babu abinda take buƙata sama da haɗin kai daga wurin mutanen da suke gudanar da ita. Babu yadda za a yi cigaba ya samu matuƙar irin waɗannan abubuwa suna faru.

Gwamnati Buhari ta zo da manufofi masu kyau waɗanda za su ɗora ƙasar nan kan turbar gaskiya, amma rahin haɗin kai tsakanin jami’anta na cikin babban tarnaƙin da take fuskanta, wanda ya kamata a kawo ƙarshensa cikin gaggawa, ko da kuwa ta kama sai wasu sun rasa kujerunsu ne.

Ya kamata a koyi darasi kan taƙadama da taɓa shiga tsakanin Ministan Shari’a Abubakar Malami da kuma Muƙaddashin Shugaban Hukumar EFCC Ibrahim Magu, koda yake daga baya sun musanta zargin.

Har ila yau, irin wannan ta shiga tsakanin Ministan Lafiya da kuma shugaban hukumar NHIS, wanda sai da ta kai ga dakatar da shugaban hukumar da kuma kafa kwamitin bincike kan al’amarin.

A wannan gaɓar, ya kamata a ce Shugaba Muhammadu ya shigo tsakiya domin yi wa tufkar hanci.

 

Exit mobile version