Bello Hamza" />

Badakalar Biliyan 11: An Sa Ranar Sauraren Shari’ar Shema

Babban kotun Katsina ta sanya ranar 10 zuwa 12 ga watan Afrilu na wannan shekaran domin ci gaba da sauraron shari’ar tsohon gwamnan jihar Katsina Ibrahim Shema da wasu mutum 3 a kan zagin sama da fadi da Naira Biliyan 11 da ake musu.

Wannan ya biyo bayan hukuncin kotun koli ne in data yanke na cewa, tsohon gwamnan Ibrahim Shema tare da Hamisu Makana tsohon kwamishinan kananan hukumomi da Ahmed Rufai Safana tsohon babban sakatare da kuma Ibrahim Lawal Dankaba tsohon shuganan kungiyar kananan hukumomin  na jihar su gabatar da kansu ga babban kotun jihar domin ci gaba da sauraron tuhumar da ake yi musu, koma bayan bukatar tawagar lauyoyin tsohon gwamnan in da suka bukaci a yi wasti da shari’a daga babban kotu saboda bata da hurumin sauraron karar.

Alkalin dake gudanar da shari’ar, Mai Shari’a Ibrahim Maikaita Bako, ya daga shari’ar zuwa ranar da aka aiyyana, gwamnatin jihar Katsina da Hukumar EFCC ce suka shigar da karar wadanda ake zargi a gaban kotun.

Tuni dai kotu ta bayar da beli Shema da sauran wadanda ake zargi kafin su garzaya kotun daukaka kara da kotun koli domin a tabbatar musu da hakkinsu na dan Adam.

A zaman da ya gudana ranar Talata, lauyoyin gwamnatin jihar da na EFCC wanda Ahmed Usman El-marzuk da Sam Ologunorisa (SAN) suka jagoranta sun nemi a kotu ta basu daman yin gyara a takardar da suka shigar a ranar 24 ga watan Maris 2017.

Da yake gabatar da bukatar tasu, Ologunorisa (SAN) ya bayyana wa kotun cewa, dalilan su na neman yin gyaran na nan a takardar da suka mika wa hukumar kotun ta hannun M. S. Abubakar.

Lauyoyin da ke kare wadanda ake kara wanda Joseph B. Dauda ke jagoranta ya ki amincewa da bukatar da masu gabatar da kara suka mika wa kotu, sun kuma bukaci daga sauraron karar zuwa wani lokaci.

Da yake yanke hukunci, bayan an yi hutun mintin 10, Mai Shari’a Bako ya bukaci lauyoyin masu gabatar da karar su janye bukatan su ta 3 a takardar da suka mika wa kotu, abin da nan take Ologunorisa (SAN) ya yi Lauyan mai kare wadanda ake zargi ya ce bashi da matsala da janyewar da aka yi. Daga karshe mai shari’a Bako ya cire bukatar da ake magana a kai ya kuma dage karar zuwa lokacin da aka aiyyana a baya.

Exit mobile version