Badakalar Kasafin Kudi: Majalisar Wakilai Ta Dage Dakatarwar Da Ta Yi Wa Jibril

Daga Abdullahi Usman, Abuja

Majalisar wakilai ta tarayya ta daje dakatarwar da ta yi wa tsohon shugaban kwamitin kasafin kudo na majalisar wakilai, Dan majalisa Abdulmumin Jibril.

Jibril wanda aka dakatar har na tsawon kwanakin aiki na majalisar 180, a watan Satumbar 2016, Jibril, Jibril dai ya kwashe sama da shekara daya da wata hudu ba tare da ya shiga majalisar wakilai din ba, saboda wannan dakatarwa da aka yi masa, sai a ranar talata bayan an dage wannan dakatarwa.

Dan majalisar dai, wanda ya fito daga jihar Kano ya nemi gafarar takwarorinsa na majalisar kan zargin da ya yi a wancan lokaci na sama na naira biliyan40 da ya ce an sakasu a kasafin kudi. Wanda hakan ya jawo majalisar ta dakatar da shi.

Shugaban majalisar, Mista Yakubu Dogara ne ya daga wata wasika a zaman majalisar, da ya bayyana da cewa Abdulmumin Jibril ne ya aiko da sakon baiwa majalisar hakuri kan abin da ya yi. Dogara dai ya bayyana cewa ba da hakurin da Jibril ya yi na daga cikin abin da majalisar ta nema kafin dawowa da shi cikin majalisar.

“Wannan takarda ta ba da hakuri da Jibril ya yi, ya nuna cewa ya cika ka’idojin da aka shimfida masa. Saboda haka zai iya dawowa zaman majalisar, face kuma ya sake aikata wani abin na daban.

A shekarar 2016 ne Dogara ya kori Jirbil daga shugabancin kwamitin majalisar wakilai na kasafin kudi, wanda ake jin ba zai rasa nasaba da badakalar kasafin kudi ba.

Wasu daga cikin wadanda Jibril ya zarga da wannan aiki sun hada da Mataimakin shugaban majalisar, Yusuf Lasun, mai tsawatarwa, Alhasana Ado Duguwa da kuma shugaban marasa rinjaye Mista Leo Ogar.

Jibril kuma ya yi zargin cewa wasu ‘yan gata a majalisar an sanya masu kudade a cikin kasafin kudin. Sannan ya yi kira ga shugabannin majalisar da su sauka daga mukamansu, sannan EFCC ta hukunta su kan almundahana din da suka aikata.

Daga baya majalisar ta bincike Abdulmumin Jibril, sannan ta fitar da cewa ya kunyata majalisar kan wannan almundahanar da ya yi zargi.

Daga baya kuma majalisar gaba daya ta amince da dakatar da shi na tsawon kwanaki 180 na zaman majalisar.

Ofishin dan majlisar dai ya bayyan cewa dan majalisar zai dawo aiki jiya laraba.

 

Exit mobile version