Connect with us

Uncategorized

Badakalar Miliyan 500: EFCC Ta Cafke Mukhtar Shagari

Published

on

Hukumar EFCC ta gyrfanar da tsohon ministan ruwa Mukhtar Shagari tare da wasu mutane uku a gaban mai shari’a Idrissa Kolo na kotun tarayya dake Sokoto a bisa tuhuma 5 na hadin baki da almundahana na Naira Miliyan 500.

Wadanda aka tuhuma tare da tsohon ministan sun hada da Abdullahi Wali da Ibrahim Gidado da Nasiru Bafarawa da kuma Ibrahim Milgoma.

Batun ya taso ne a yayin da hukumar EFCC ta samu bayanan sirrin cewar, wadanda ake zargin sun karbi kaso daga cikin Dala Miliyan 115 da tsohuwar ministan man fetur, Misis Deizani Allison Madueke ta raba wa manyan ‘yan jam’iyyar PDP da wasu jami’an hukumar zabe ta INEC domin su jirkita sakamakon zaben shugaban kasa na shekarar 2015.

Wadanda ake zargin su amfana daga cikin kason naira Miliyan 500 da aka raba musu ba ta hanyar wani cibiyar huldar kudi ba, abin da yin haka ya saba wa dokan yaki da cin hanci da rashawa.

Daya daga cikin takardar tuhumar yana cewa, “Kai Mukhtar Shehu Shagari da Ibrahim Gidado da Ibrahim Milgoma a wani lokaci a cikin watan Maris na 2015, a yakin da wannan kotun ked a hurumi kun hada ka a tsakaninku kuka karbi naira Miliyan 500 daga hannun wani mai suna Abdulrahaman Ibrahim ba tare an huldar ta hannun wata cibiyar kudi da hukuma ta yarda das u ba hakan kuma laifi ne  a karkashin sashe na 18(a) na dokan cin hanci da rashawa hukuncin wannan laifin kuma yana a sashe na 16 (2) kamar dai yadda aka gyara a shekarar 2011”

Dukkan wadanda ake zargin sun musanta aikata laifin, bayan an karanto musu.

Lauyan masu gabatar da karar Mista Ojogbane, ya nemi a sanya ranar da za a ci gaba da sauraron karar kamar dai yadda wadanda ake zargin suka nema, amma ya nemi kotu ta bayar da izinin ci gaba da tsaresu a gidan yari har zuwa ranar da za a ci gaba da saurarar karar.

Lauyan dake kare wanda ake zargi na daya dana uku Ibrahim Abdulaziz tare da lauyan dake kare wadanda ake zargi na biuu dana biyar Ibrahim Idris da L.A Abdulkadir sun gabatar neman belin wadanda ake zargin kafin a yanke hukuncin karar.

Da yake mayar da martini, Mista Ojogbane, ya tabbatar da cewar, an bashi takardar neman beli, amma a jiya (21 ga watan Mayu) ne aka bashi takardar a saboda haka yana bukatar lokaci kafin ya bayar da amsa.

Bayan da Mai shari’a Idrissa, ya saurari masu gabatar da bukatar belin, ya umuci a tasa keyar wadanda ake zargin zuwa gidan yari har zuwa ranar Alhamis 24 ga watan Mayu 2018, lokacin da zai yanke hukunci a kan bukatar belin.

 
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: