Bello Hamza" />

Badakalar Naira Biliyan 10 A NHIS: Jam’iyyar PDP Ta Caccaki Gwamnatin Buhari

Jam’iyyar PDP ta ce, gwamnatin Muhammadu Buhari ta zubar da mutuncin ta yayin da ta ke kokarin boye satan Naira Biliyan 10 da aka tafka a Hukumar Inshoran Lafiya ta kasa NHIS. Jam’iyyar ta ce, a halin yanzu tsananin rashin iya aikin gwamnatin Buhari sai kara bayyana ya ke yi.

A sanarwar da jami’in watsa labaran jam’iyyar ta kasa Kola Ologbondiyan, ya sawa hannu, ta ce al’amarin na da ban tsoro in da ake satar kudade daga asusun TSA dake babban bankin kasa na CBN wanda dukkansu na karkashin ofishin shugaban kasa ne.

“A halin yanzu ‘yan Nijeriya sun fahinci tsananin almundahanan da ake tapkawa a wannan gwamnatin in da Shugaba Buhari ke jagorantan satar da ake tafka wa a bangarori daban daban na gwamnati”

“Muna kalubalantar ofishin shugaban kasa su fito su yi bayani a kan wannan rahoto na satar da aka tafka a NIHS da sauran irin su da aka yi cikin wannan gwamnatin.

“Wane ne a ofishin shugaban kasa ya bayar da izinin fitar da kudin daga asusun TSA kuma su wa suka amfana da kudaden satar” “Mene ne ofishin shugaban kasa zai ce game da bayanan cewa su suka bayar da izinin dawo da shugaban Hukumar NIHS Farfesa Yusuf Usman bakin aiki saboda a boye satar da aka tafka, ya kuma kare wasu jami’ia a ofishin shugaban kasa dake da hannu a badakalar” “Dole ofishin shugaban kasa ta wanke sunanta, ta hanyar gudanar da bincike da kuma hukunta wadanda suke da hannuna a satar da a ka tafka” “Laifin halin talauci da tsananin yunwan da kuma macemace da ake fama da shi a Nijeriya na a kan gwamnatin APC”

Jam’iyyar PDP ta kuma nuna rashin jin dadin ta a kan yadda shugaba Buhari ya ki daukan mataki bayan da rahoto ya nuna an yi sama da fadi na kudade har Naira Biliyan 9 daidai da Dala Biliyan 25 a kanfanin mai  a NNPC wanda ke karkashin ofishin Shugaba Buhari kai tsaye.

“’Yan Nijeriya na sane cewa, shugaba Buhari na ci gaba da kange ‘yan majalisarsa da ake zargi da hannu a satar kudaden jama’a”

Jam’iyyar ta kuma ki yarda da bayanin Ministan watsa labarai Alhaji Lai Mohammed in da ya ce, wai kasar nan na a amintaciyar hannu, kuma bayan haka kasar nan na cikin halin tabarbarewa ne a bangarori daban-daban, saboda rashi kwarewar wadanda suke tafiyar da harkokin kasar nan a halin yanzu ‘yan Nijeriya na cikin matsanancin hali.

PDP ta nuna kaduwar ta a kan bayanin da Ministan ya yi, domin kuwa ‘yan Nijeriya na nan na dandana wahalhalun da gwamnatin shugaba Buhari ta tsundumasu sakamakon tsatsauran matsanancin tattalin arziki da ake ciki.

Sanarwar jam’iyyar PDP ta ye, Minista Lai Mohammed bai san halin da ‘yan Nijeriya ke ciki ba ko kuma yana son boye rashin iya aikin Buhari da jam’iyyarsa dake fama da tsananin rikice-rikice.

Jam’iyyar ta nuna tausayawanta ga Ministan watsa labaran a kokarinsa na tallar gwamnatin da ta gaza a aiyukanta, sai ta shawarce shi daya kauce wa fadan karya a yayin gudanar da aiyukansa.

“In ministan watsa labarai da ake sa ran zai bayar da bayanai na hakika a kan kasa zai bige da yabon gwamnatin da ta jefa tattalin arzikin kasar nan cikin rudu ta kuma haifar da rikice-rikicen siyasa da na addini to lallai lamarin na da ban tsoro”

Exit mobile version