Kotun daukaka kara da ke da zamanta a babban birnin tarayyar ta tabbatar da hukuncin da Mai Shari’a Alkali Okon Abang na kotun tarayya da ke a Abuja ta yanke a ranar 19 ga watan Yulin 2021, inda ta umarci tsohon gwamna Jihar Adamawa Adimiral Murtala Nyako mai murabus da ya gabatar da kariya a ci gaba da tuhumar da ake yi masa.
Hukumar yaki da cin hanci da rashawa da yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa (EFCC) ce ta gabatar da karar ta tshon gwamnan, ‘ya’yansa biyu, wasu kamfanoni da ake kira da Sebore Farms, Edtension da kuma Pagado Fortunes bisa zargin yin safarar kudade ba bisa ka’ida ba
Sauran wadanda za su kare kansu a gaban kotun sun hada da, Zulkifik Abba, Abubakar Aliyu, kmfanonin Blue Opal Tower, Assets Management da kuma Crust Energy. Idan za a iya tunawa dai, a ranar 7 ga watan Yulin 2015 ne EFCC ta shigar da karar a kan Nyako da sauran wadanda ake tuhuma.
Da yake yanke hukuncin kan hukuncin da kotun daukaka kara ta yi bisa kalubalantar korar karar, Mai Shari’a Olabisi Ige tare da sauran alkalai uku ya bayyana cewa, wadanda za su kare kansun na da damar shigar da kariya domin su amsa tambaya.