Connect with us

Uncategorized

Bagen Tumatir Na Iya Haifar Da Cutar Kansa –NAFDAC

Published

on

Hukumar NAFDAC ta gargadi al’umma da su guji amfani da rubabben tumatir wajen yin girki, domin yana dauke da kwayoyin cutar da za su iya haifar da cutar kansa a jikin dan Adam, duk tumatir din da ya rube ya yi hunhuna yana iya zama dauke da wasu kwayoyin cuta wanda suke iya juyewa su zama kwayar cuta mai suna ‘Mycotoxins’

‘Mycotoxins’ suna da matukar hadari a jikin dan Adam, mafi yawan mutane suna ganin bagen tumatir bashi da wata matsala musamman in an wanke shi an dafa shi, ga shi kuma yana da arha ba kamar mai kyau ba.

Mataimakiyar Direkta a hukumar mai suna Christiana Essenwa tana ce: Lallai wanke bagen tumatir ko dafa shi akan wuta ba zai kashe kwayoyin cutar ‘Mycotoxins’ ba wadanda suke jawowa dan Adam kamuwa da cutar kansa, mafi alheri kawai mutane su guji amfani da bagen tumatir din, gwara a dinga daurewa ana siyan mai kyau duk tsadar shi, saboda kiyaye kamuwa da cutar kansa.
Advertisement

labarai