Daga Umar Faruk Birnin Kebbi
Gwamna Abubakar Atiku Bagudu ya amince da bayar da Naira miliyan hudu da dubu dari takwas ga ‘yan jihar Kebbi don halartar atisayen daukar aiki na sojen jirgin sama na Nijeriya a Mundo da ke a Jihar Kaduna.
A cewar wata sanarwa da Sakataren gwamnatin jihar Kebbi, Babale Umar Yauri ya sanya wa hannu, ‘yan jihar Kebbi dari da casa’in (190) ne za su yi halarci ofishin hukumar sojojin jirajen Saman Nijeriya da ke a Jihar Kaduna don neman a dauke su aikin.
‘Yan jihar ta Kebbi wadanda za su mallaki takardun ND, NCE, SSCE da wadanda ke da takardar shaidar kasuwanci ne suka kama hanyar zuwa Jihar ta Kaduna.
Gwamnan a cikin tausayinsa na inganta walwalar al’ummar jiharsa, ya amince da bayar da Naira dubu ashirin (N20,000) ga kowane dan Jihar ya halarci Kaduna.
Gwamna jihar, Sanata Abubakar Atiku Bagudu ya tabbatar da kudurinsa na rage rashin aikin yi a tsakanin matasa tare da bukatar cika dukkan gurabun jihar a dukkannin ayyukan daukar sabbin ma’aikata a duk fadin ma’aikatun gwamnatin Tarayya, da sauran wasu hukumomin.
Daga karshe, ya ja kunnuwan ‘yan Jihar da su kasance jakadu na gari, su kuma mayar da hankalinsu ga abin da suka je nema. Ya kuma yi musu fatar al’hairi.