Bagudu Ya Amince Da Tallafin Naira Miliyan 4.8 Ga ‘Yan Jihar Kebbi Don Su Halarci Daukar Ma’aikata Na NAF

NAF

Daga Umar Faruk Birnin Kebbi

Gwamna Abubakar Atiku Bagudu ya amince da bayar da Naira miliyan hudu da  dubu dari takwas ga ‘yan jihar Kebbi don halartar atisayen daukar aiki na sojen  jirgin sama na Nijeriya a Mundo da ke a Jihar Kaduna.
A cewar wata sanarwa da Sakataren gwamnatin jihar Kebbi, Babale Umar Yauri ya sanya wa hannu, ‘yan jihar Kebbi  dari da casa’in (190) ne za su yi halarci  ofishin hukumar sojojin jirajen Saman Nijeriya da ke a Jihar Kaduna don neman a dauke su aikin.

‘Yan jihar ta Kebbi  wadanda za su mallaki takardun ND, NCE, SSCE da wadanda ke da takardar shaidar kasuwanci ne suka kama hanyar zuwa Jihar ta Kaduna.
Gwamnan a cikin tausayinsa na inganta walwalar al’ummar jiharsa, ya amince da bayar da Naira dubu ashirin (N20,000) ga kowane dan Jihar ya halarci Kaduna.
Gwamna jihar, Sanata Abubakar Atiku Bagudu ya tabbatar da kudurinsa na rage rashin aikin yi a tsakanin matasa tare da bukatar cika dukkan gurabun  jihar a dukkannin ayyukan daukar sabbin ma’aikata a duk fadin ma’aikatun gwamnatin Tarayya, da sauran wasu hukumomin.

Daga karshe, ya ja kunnuwan ‘yan Jihar da su kasance jakadu na gari, su kuma mayar da hankalinsu ga abin da suka je nema. Ya kuma yi musu fatar al’hairi.

Exit mobile version