Connect with us

Uncategorized

Bahaushe: Allah Ya Maido Da Hankalin Mai Tafiya

Published

on

Daya daga cikin dalilan da yasa yau a kasar Hausa muke cikin matsaloli daban-daban na zamantakewa shi ne yadda mu ka yi watsi da wasu kyawawan dabi’unmu na zamantakewa.
Wani masanin tarihi mai suna Dokta Mustapha Muhammad Gwadabe wanda malami ne a jami’ar Ahmdu Bello dake Zariya, ya taba wallafa wata mukala akan yadda tsarin mallakar kasa yake a kasar Kano kafin zuwan turawa.
A cikin wannan mukala, ya nuna cewa a wancan lokaci, kowane iyali ko zuri’a, na da ikon ta yanki iya adadin kasar da tai mata, musamman gona ko gonaki, da za sui amfani dasu domin su samu abinci. A zamanin ba a sayar da kasa, ko a bada ta haya ko jingina. A’a kasa na nan wadatacciya. A cikin wannan mukala, ya fito da yadda tsarin gandu yake ,inda iyalai kan hada kai su nome gonakansu, kuma in lokacin girbi ya yi su girbe su zube a rumbu guda. Duk wani wanda ke bukatar abinci a gidan to daga wannan babban rumbu ne za a debo a bashi. Akwai kuma al’adar aikin gayya, inda za a gayyato mutane da yawa su zo su gudanar da noma ko girbi ko roro a gona. Kowa nada damar da zai bada goron gayya domin a zo a taya shi nashi aikin. Wannan aikin na taimakawa mutum ya noma wuri mai girma domin kara samun yalwa .Sai dai a cikin wannan tsari na aikin gayya, babu tilastawa a ciki. Idan mutum nada wani uzuri, to zai iya kin zuwa.
Masanin ya bayyana cewa daga lokacin da aka fara sarauta a kasar Hausa, daga lokacin ne, tsarin mallakar kasa da batun aiki ko kwadago ya canza. Masanin ya kawo dalilan da suka kawo wannan sauyi da yadda wannan sauyi yai tasiri akan zamantakewar Hausawa. Ya ce kasa ta koma mallakar Sarki, kuma shi sarkin ne keda ikon ya bada ta ko ya amshe ta. Sarakuna suna bukatar kasa saboda inda za su tsugunnar da matayensu, kuyangansu (Misali an ce sarkin Kano Yaji yana da kuyangai sama da dubu), suna bukatar inda za su tsugunnar da bayinsu. Kazalika, suna bukatar manya-manyan gonakai da yawa domin noma abinci isasshe. Kazalika idan baki sun zo, sarki ne zai ba shi wurin zama da gonar da zai dinga nomawa.A cikin karni na sha-bakwai da na sha-takwas, tsarin sarauta ya kara fadada inda ke akwai ofisoshi daban-daban dake karkashin sarki, ga masu gari, hakimai da dagatai da sauransu. Duk wannan na nuni nufin karin bukatar kasa.
Daga wannan lokaci ne aka fara yi ma sarakunan da lakabin ‘masu kasa’. Daga nan, sai kuma Sarakunan suka fara kuntatawa talaka inda sukan kwace ma gona ko gonaki. Misali, a karni na sha takwas, Gobir ta mamaye Zamfara kuma ta kwace gonaki da dama daga hannun Zamfarawa. Kusan kwacen gonaki da sarakunan kasar suke a wancan lokaci, ya taka rawa wajen sanyawa Hausawa talakawa su mara ma Shehu Usman Dan fodiyo baya ya yaki sarakunan Hausawa lokacin jihadi.
Baya ga kwacen gonaki, akwai kuma aikin tilas. Sabanin a da, inda ba tilas a aikin gayya. Lokacin sarauta, akan tilasta ma talakawa aikin gona a gonakin sarakuna, kuma duk wanda yai taurin kai, yana dandana hukunci. Wannan tsarin na aikin tilas ya ci gaba har lokacin da turawan mulkin mallaka suka zo, suka kwace mulki daga hannun sarakuna, an yi amfani da aikin tilas wajen gina layukan dogo.
Idan muka nazarci wannan takaitaccen tarihi za mu ga cewa daga lokacin da aka fara batun mallakar kasa, da sayar da ita, daga nan matsalolinmu suka fara ta’azzara. Wani masanin falsafa dan kasar Faransa mai suna Jean Jackue Russeaou ya taba cewa Mutumen farko da ya yanki wani wuri na kasa, ya ce wannan nasa ne, to shi ne tushen duk wani zalunci da annoba a duniya.A ganin wannan masanin falsafa, kasa ta Allah ce bata kowa ba. Yanzu abin da ke faruwa, a kullum kasa tsada take yi, saboda ‘yan jari hujja sun shigo sun mallake ta. Kullum dubban talakawa ne ke kara rasa gonakinsu na nomawa, ko muhallansu inda saboda yadda kasa take da daraja, tasa mutane na hada-hadarta domin biyan bukatunsu.Mun saki tsarin mallakar kasa na asali, gashi yanzu kasa ta fi karfin talaka. Masana na cewa idan mutum nasan mallakarka, to ya mallaki kasarka.
Shima aikin gayya mun sake shi, don haka, yanzu aikin kwadago tsada yake. Maimakon a da, da baka bukatar ko sisin kwabo kafin a nome ma dukkanin gonakinka saboda tsarin aikin gayya, yanzu sai dai kaki noman kwata-kwata in baka da kudi.
Tsarin zamantakewa na gandu, inda tsari ne na cudann-i in- cude- ka,zZa ka tashi a gidanku, ka ci gaba da hada kai da ‘yan uwanka, domin ku kare mutuncinku, yanzu an watsar da shi. Kowane yaro, ya gwammace ya tai Anaca ko Lagos ko Aba, kwadago, Acaba ko wankin takalmi. Daga karshe meke faruwa? Ba wan ba kanen. Ba ai arzikin ba, kila ma a kwaso cuta ko wani mugun hali. Amma a da lokacin da ake zaman gandu, Baya ga wadata, akwai tarbiyya, domin kodayaushe mutum na nan kusa da mahaifansa, kuma suna lura da dabi’unsa na yau da kullum, sannan duk shekarunsa, in yai abin laifi, bai wuce a kira shi ai mai fada ba. Mutum zai koyi yadda mahaifanasa ke zamantakewa ciki har da ta auratayya. Saboda haka, lokacin da akai mai aure, aka gina mai dakinsa gefe guda, to iyayensa za su ci gaba da kula da shi da amaryar. Wannan yasa aure bai sauran mutuwa. Amma yanzu mutumen da baida gogewa ta zaman duniya, ya je ya yi aure ko shawara cikakkiya bai yi da mahaifansa ba, ai dole aure ke mutuwa a banza.
Idan zamani yasa watakila ba za mu iya canza tsarin mallakar kasa ba, to kuma yaya za ai a ce ba zamu iya zamanantar da tsarin zamantakewa na gandu ba? Don mi ya sa za mu yi ta kwaikwayon turawa cikin har da tsarin zamantakewarmu da gine-ginenmu?
Koda a baya-baya cikin shekarun alif dari tara da tamanin zuwa da casa’in, za ka samu wasu kyawawan al’adun da yanzu mun daina su . Misali, fito da abinci waje, inda yaran unguwa kowa zai fito da abincin da aka dafa gidansu a taru a ci. In an ci na wannan, an gama, a koma a ci na wannan har sai an koshi sauran a ba almajirai. Amma yanzu an daina an koma rowa. Hatta kakaninmu da iyayenmu a wancan lokaci waje suke cin abinci da makwabta, amma yanzu an daina. Kowa cikin gida yake cin abincinshi,kowa tasa ta fisshe shi.
Haba Mallam Bahaushe ba a sanka da rowa ba, kai ba marowaci ba ne. Bature ne marowaci wanda ko gidansa in an je an iske yana cin abinci yana iya hanawa ya ce, ba a gaya masa cewa za a zo ba.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: