Bai Kamata Amurka Ta Yi Biris Da Karfin Masu Matsakaicin Kudin Shigar Al’ummar Sinawa Ba

Daga CRI Hausa

Jaridar South China Morning Post ta ba da bayani cewa, karuwar alummar Sinawa masu matsakaicin kudin shiga dake birnin Shanghai sun karyata jita-jitar da Amurka ta yayata wai Sin tana kawo barazana ga duniya.

A ganin marubucin bayanin, bai kamata Amurka ta yi biris da karfin wadannan mutane, kuzari da kuma karfinsu na kalubalantar tunanin kasashen yamma wai Sin tana kokarin yayata tunaninta da hanyarta na samun bunkasuwa ga duniya ba.

Bai kamata kasashen yamma su dauki manufar tsattsauran raayin kishi irin na Amurka don nuna wariya da nisantar wadannan mutane ba, matakin da zai lahanta moriyar kasashen yamma har ma da na duniya baki daya. (Amina Xu)

 

Exit mobile version