Connect with us

KIWON LAFIYA

Bai Kamata Ka Zuba Fitsari Ko Ruwan Nono A Idonka Da Ke Ciwo Ba -Masana

Published

on

Abin yabi jikin wasu wajen sanya wa idanuwan su wasu hade-hade idan suna jin zafi ko kuma suna fama da wasu matsalolin ido.

Wani kwararren likitan ido Dakta Echendu Damian, ya shawarci mutane masu yin dabi’ar dasu bari don gudun kadasu jefa iadnuwan su a cikin matsala harda ta makanta, inda ya ce, mutane su dai na zuba fitsari, ruwan nonon mace, kalanzir ko kuma wasu sanadarai da ka iya haifar wa da idanuwan su matsala.

Dakta Echendu wanda kuma shi ne shugaban kungiyar likitocin ido ta kas (NOA), ya shawarci mutane da su daina sayen tabarau a wurin wadanda ba kwararru akan ido ba, inda ya ce, mutane su dinga zuwa asibiti wadanda za su duba su yadda ya kamata da kuma basu tabarau da ya dace da idanuwan su.

A cewar sa, ido yana da mahimmanci sosai kuma ba abune da za’a iya chanza shi ba kamar yadda ake chanza kafa ko hannu ba ko kuma sauran wasu sassan jiki ba.

Ya kuma shawarci mutane dasu dinga zuwa asibiti ana duba lafiyar idanuwan su a kalla sau daya a shekara ya kuma shawarce su dasu dinga yin amfani da tabarau mai rage karfin rana ba kuma su dinga saye a shaguna ba amma su tabbatar da sun je gun kwararru don auna su da tabarau din da ya dce dasu.

Ya yi kira ga gwamnati data samar da isassun kayan aiki da kuma kwararrun ma’aikatan ciwon ido,inda ya ce akan karacin ma’aikatan ciwon ido a asibitocin gwamnati da kuma a kananan hukumomi.

Da yake Magana akan bikin kungiyar karo na 42 Dakta Echendu ya ce, wadanda aka yaye masu kula da lafiyar ido suna fuskantar rashin daukar su aiki.

A cewar sa, kungiyar tana da wadanda suka yi rijista har 4,000 a kasar nan duk da gudunmawar da suke bayarwa a fannin kiwon lafiya amma gwamnati tana daukar yan kalilan daga cikin su ne.

Ya kara da cewar, hakan ya sanya sama da kashi  80 suke yin aiki a asibitoci masu zaman kansu wasu kuma suke tafiya zuwa kasar Saudiya da Bitaniya da sauran kasashe, inda suka kai har su 3,200.

A cewar sa, kungiyar tana kuma wayar da kan mutane akan yadda za su kaucewa makanta, musamman a tsakanin yara daga shekara biyar zuwa sha hudu.

A karshe ya ce, kungiyar a kwanan baya ta yi hadaka da da hukumar kiyaye hadurra (FRSC) don gudanar da bincike a kan idanuwan direbobi don samar da tsari a kasar.

 
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: