Bai Kamata Magoya Baya Su Yi Wa Benzema Ihu Ba, In Ji Ronaldo

Dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid, Cristiano Ronaldo ya bayyana rashin jin dadinsa ga magoya bayan kungiyar bayan da suka yiwa dan wasa Karim Benzema ihu  a wasan da kungiyar ta doke Real Soceidad daci 5-1 a ranar Asabar din data gabata a wasan laliga.

Dan wasa Benzema ya zubar da wata dama ta zura kwallo a raga a lokacin da kungiyar take kan gaba da kwallaye biyar amma duk da haka magoya bayan kungiyar basu dagawa Benzema kafa ba suka dinga yimasa ihu saboda zubar da wannan damar.

Sai dai dan wasa Ronaldo yace abinda magoya bayan kungiyar sukayiwa Benzema baiji dadinsa ba kuma bai kamata ba saboda ya zura kwallaye da dama a kungiyar a baya kuma yanzu ma yana iya kokarinsa wajen ganin ya farantawa magoya bayan kungiyar rai.

Ya kara da cewa yakamata magoya bayan kungiyar su gane komai yanada lokaci kuma burin dan wasan gaba shine ya zura kwallo a raga.

Suma yan wasan kungiyar, Marcelo da Toni Kroos sun nuna rashin jin dadinsu ga halayyar magoya bayan inda sukayi kira ga magoya bayan kungiyar dasu cigaba da goyawa  yan wasan  kungiyar baya.

Real Madrid dai zata buga wasanta na gaba da kungiyar kwallon kafa ta Paris Saint German a gasar zakarun turai a ranar Laraba a filin wasa na Santiago Barnabue dake kasar sipaniya.

 

Exit mobile version