Bai Kamata A Rage Darajar Yaki Da Cin Hanci Da Rashawa Ba —Sanata Makarfi

Shugaban kwamitin riko na Jam’iyyar PDP ta kasa, Sanata Ahmed Muhammed Makarfi, ya tattauna da wakilinmu ABUBAKAR ABBA, inda ya yi karin haske game da shirye-shiryen da jam’iyyar tasa ke yi na aiwatar da wani babban taro na kasa nan ba da jimawa ba, tare da yin sauran bayanan da suka shafi al’amuran kasa. Ga yadda hirar ta kasance:

Mai girma Sanata, wane shiri kuke aiwatarwa a halin yanzu dangane da babban taron da kuka sanya a gaba na Jam’iyyarku ta PDP a Kasa?

Alhamdulillahi! A halin da ake ciki yanzu taron namu ya dan samu tsaiko sakamakon karin watanni hudu da aka yi. Hakan ya kara tabbatar mana da matsayar da kwamitin rikon kwaryar na Jihar Anambara suka cimma matasaya a kai, bayan rusa dukkanin bangarorin y’an taware na jam’iyyar tare da kafa sabbin kwamitoci don gudanar da zaben Gwamna mai zuwa a Jihar ta Anambara. Kazalika taron zai kara tabbatar da hukuncin da Kotun koli ta zartar a kwanakin baya.

Haka nan taron zai rusa dukkanin y’an taware na jam’iyyar da ke wasu jihohi da kuma sauran guraren da aka kasa samun masalaha ko matsaya na rikice-rikice a Kasa baki daya. Wadanda kuma suka ki yarda a samar da masalaha a tsakanin su, Jam’iyyar za ta yi amfani da karfin ikon taron don  rusa y’an  taware ko y’an tawaye na Jam’iyyar ta PDP don samar da zaman Lafiya mai dorewa da kuma jan kowa a jiki don ganin an  gudu tare an kuma tsira tare.

Haka zalika, taron zai taimaka wajen samar da hanyar da za a zabi nagartattun Shugabannin Jam’iyyar na Kasa a zaben da za a yi a watan Disamba.

Ina tabbatar maka da cewa, a irin rahotannin da nake samu a halin yanzu,  mafi yawancin y’an taware na wannan Jam’iyya tamu, sun yafewa junanansu kuma sun hada kansu waje guda.

 

Wane irin shiri kuka yi don ganin an tabbatar da an zabi Shugabannin Jamiyyar na gari a taron naku mai zuwa?

Ko shakka babu, har yanzu muna nan a kan matsayinmu na ganin cewa kujerar Shugabancin Kasar nan ya ci gaba da zama a Arewa, ba mu kuma ware wani bangare a Arewar ba da ya kamata kujerar Shugaban Kasar ta koma ba.

Amma muna nan a kan bakanmu na barin Shugabancin jam’iyyar ya kasance a kudancin wannan Kasa, kazalika ba mu ce ga yankin da ya kamata su fitar da Shugaban jam’iyyar na Kasa ba. Manufarmu a nan ita ce don mu bude kofa a inda daga karshe za mu samu Shugaban da kowane dan jamiyyar tamu zai yi na’am da shi.

Tun kafin mu gudanar da wannnan taro namu kasa, tuni mun kaddamar da kwamitocin sasanta y’ay’an wannan Jam’iyya ta PDP da aka batawa a baya, da kuma kaddamar da kwamitin ladabtarwa. Babu shakka aikin wadannan  kwamitocin yana da fadin gaske, kuma Alhamdulillahi don kuwa suna samun dimbin nasarori a kan wannan nauyi da aka dora musu. Haka nan kuma, an kaddamar da kwamitin ladabtarwanne ba tare da nufin muzgunawa y’ay’an jam’iyyar ba. An yi hakan ne domin duk abinda babu ladabi a ciki, ba zai taba yin karko ba.

Ba wai muna son mu takurawa y’ay’an PDP ba ne, amma muna son dukkanin y’an jam’iyyarmu su bi hukuncin da Kotun koli ta yanke, illa iya ka idan an tabbatar da dan jam’iyyar ya yi wa jam’iyyar zagon kasa, za a hukunta shi kamar yadda kundin tsarin mulkin jam’iyyar ya tanada da kuma na dokokin kasa.

 

Ka mayar da kujerar Shugabancin Kasar nan ga Arewa, amma wasu Shugabanni daga kudancin Kasar suna korafi, ba ka ganin wannan matakin ya sabawa kundin tsarin Jam’iyyar taku?

Ko daya, wannan dama shi ne matsayar da jamiiyar ta yanke. Sannan zan so na yi amfani da wannan damar in sake jaddada cewa, har yanzu matsayinmu na barin kujerar Shugaban Kasa a Arewa yana nan daram- dam bai canza ba. Matsaya ce da aka yanke lokacin taronmu Kasa da aka gudanar a ranar 21 ga watan Mayu, a garin Fatakwal kuma wannan matsayar na kan kowane dan Jam’iyyar PDP. Bari in kara tuna maka cewa, lokacin da aka maido da kujerar Shugaban kasa zuwa Arewa a Shekarar  1999, wasu y’an Arewa sun tsaya takara  amma daga baya PDP ta ci gaba da matakin da ta dauka tun da farko.

 

Idan aka yi la’akari da yanayin lafiyar Shugaba Buhari, kana ganin zai iya jurewa kalubalen ci gaba da mulkin kasar nan?

Jamiyyar PDP  ta fitar da bayanai da dama a kan cewa, Allah Ya ba shi lafiya, kuma kar ka manta, har Gwamna  Nyesom Wike ya je filin sauka da tashin jirage don yiwa Shugaba Buhari lale marhaban. Ka tuna Buhari ne Shugaban kasa har yau di nan, ba wai Shugaban   APC ba, kada ka kalli abin ta wata fuska daban. Bai kamata mu kasance masu wani mugun tunani ga  dan Adam kuma dan uwanmu ba, domin a kullum muna yiwa kowa kyakkyawan zato ko dan PDP ne ko   APC ko dan   jam’iyyar Labour ne ko dan koma dai wace jam’iyya mutum yake yi. Sai dai ba za mu iya daina sukar gwamnati ba, musamman a kan kudurorinta da basa tafiya, amma ba za mu yiwa kowa fatan gamuwa da ciwo ba. Za mu ci gaba da yiwa Shugaba Buhari addu’ar kara samun lafiya. Na biyu kuma shi ne, duk wadanda suka gudanar da zanga-zanga lokacin da Buhari ya tafi Landan neman lafiya, PDP ba ta dauki nauyin kowa ba, duk da cewar kowane dan Kasa kundin tsarin mulkin ya ba shi damar ya fito ya fadi albarkacin bakinsa. Ko a lokacin idan mutane suka zo gurinmu, muna ba su shawarar illar yin zanga-zangar, domin yau mutum zai iya wayar gari yana da lafiya gobe kuma ya kasance ba shi da ita.

Kundin tsarin mulkin kasa ya baiwa Shugaban kasa damar mika Shugancin riko, kuma Buhari ya yi hakan ta hanyar baiwa mataimakinsa rikon kasar, kuma ko mu a PDP mun tabbatar da Shugaba Buhari ya baiwa mataimakin nasa cikakken iko har sai da ya dawo gida Nijeriya. Mun fitar da sanarwa a lokacin cewa, kada mu rika yin babatu a kan rashin lafiyar ta Buhari, mu fi maida hankali wajen addu’ar Allah Ya ba shi lafiya.

 

An zargi PDP da daurewa cin hanci da rashawa gindin a Kasar nan, wanda ya yi sanadiyyar lalacewar abubuwa da dama, me yasa ka bar y’a y’an PDP da aka samu da wannan Ha’inci suka halarci taron jam’iyyar naku na Kasa?

Ya kamata ka fayyace min abin da kake son tambaya ta a fili. Koda yake  kamar maganar wani tsohon Gwamnan Jihar Neja Delta, bayan ya kammala zaman wa’adin da kotu ta yanke masa, wannan ba zai sa yaki ci gaba da harkokinsa na siyasa ba. Dokar kawai ta haramta masa yin takara ne ya zuwa wani lokaci, wannan shi ne abin da dokar ta ce. Baza mu iya tauye ma sa y’ancinsa na shigowa a dama da shi ba, domin wannan bai da wani nasaba da tsayawa takara.

Akan maganar cin hanci da rashawa kuwa, za mu tantance Gwamnatin APC ne, bayan sun sauka daga karagar mulki mu kuma mun dare a shekarar 2019, domin gaskiya za ta yi halinta. Dalili kuwa, su ma babu wanda ya fada maka cewa ba sa cikin jerin zarge-zarge don suna rike da madafun iko. Ka bari tukunna su sauka ina tabbatar maka da cewa idan muna da yawan rai, kowa zai sha kallo. Ta haka za mu san cewar ko cin hanci da rashawar da suke magana ya tsaya ne kawai a kan jam’iyya daya ko a’a. Ba mu yi adalci ba in har aka rika sanya siyasa  a kan yakin da ake yi na cin hanci da rashawa. Misali, ka dubi ma’aikatu ma su zaman kansu, su da Hukumar EFCC ta kai su kotu, babu wani wanda aka yankewa hukunci ko aka gurfanar a kotu. Idan ka ce za ka iyakance yaki da cin-hanci da rashawa a kan y’an siyasa ko kuma y’an adawa kawai, babu shakka muna ragewa yakin daraja ne.

Ya kamata a yi garanbawul gaba daya. Idan kuma na yi maka nuni da rahoton Gwamnati na Hukumar fitar da kididdiga ta kasa, wanda ya nuna fitattun ofisoshin gwamnati da aka samu dumu-dumu da cin-hanci da rashawar, kuma duk hukumomi ne na Gwamnati fa wadanda ma’aikatan Gwamnati ke jagorancin su ba wai y’an siyasa ba.

Exit mobile version