Bai Wa Baki Damar Kasuwanci A Kano Ne Sirrin Habakarsa – Sarkin Kasuwa Nafi’u

Kano gari ne da ya yi fice a harkar kasuwanci, tarihi ya nuna cewa, cudanya da baki da fatauci, da kanawan suka dade suna yi ne, sirrin habakar wannan kasuwanci, wanda kuma har yanzu kullum sai kara gaba yake.

Sarkin Kasuwar Sabon Garin Kano, Alhaji NAFI’U INDABO, ya bayyana hakan ga filinmu na Mu Tattauna. Ga cikakkiyar hirar kamar haka:

Masu karatunmu za su so ka gabatar da kanka…
Sunana Nafi’u Indabo ni ne Sarkin Kasuwar Muhammad Abubakar Rimi, wadda aka fi sani da kasuwar Sabongari, da ke Kano.


An haife ni a shekera ta 1981 a cikin birnin Kano a unguwar Yakasai da ke karamar hukumar Birni. Na yi firamari a Da’awa Primary School da ke Unguwar Lamido Crescent wadda take karkashin jagoranci Marigayi Shaikh Aminuddeen Abubakar.
Bayan na gama ta, sai na tafi makarantar gaba firamare wato, Kano Capital Secondary School da ke Nassarawa G.R.A. Bayan na kamala sakandire, sai na tafi Kwalejin Ilimi ta Tarayya F.C.E, Kano, a nan na yi diploma ta daya da ta biyu. Mahaifina Alhaji Ibrahim Nuhu Indabo,shi ne Sarkin Kasuwar Muhammad Abubakar Rimi, Marigayi Alhaji Ado Bayero shi ne ya nada mahaifina Sarkin kasuwa. Daga bisani bayan Allah ya karbi ran mahaifina a shekara ta 2012 ,sai Sarkin Kano Marigayi Alhaji Ado Bayero ya nada ni a matsayin Sarkin Kasuwa na biyu.

Ka taba shiga siyasa?

Ban taba yin siyasa ba, tun da ban taba fito wa takara ba, sai dai irin wannan siyasar ta zuciya, ka san sai mutum ya fito ya kara a zabe shi, amma zuwan da muka yi Jihar Anambra mun samu dangantaka da shi gwamnan, har gwamnan ya ce, ya kamata in fito takara, ta sanata ko ta dan majalisa.

Ganin cewa, kai dankasuwa ne, ta yaya ka iya hada siyasa da kasuwanci?
To, ita siyasa abin da ake fada, da siyasa sai dan siyasa” amma duba da yanzu zamani ya zo, shi ya sa kullum muke kallon abin da bambamcin tsari da bambamcin yanayi, ita siyasa yanzu yadda take tafiya kowa da kowa ma zai iya shiga, shi ya sa ko malamin addini ne zai iya shiga, shi ya sa ko mutum jagora ne na kowace irin kungiya zai iya shiga, saboda babu wani abu da ake a kasar nan da ya wuce siyasa.

yan siyasa su suke da ikon zartar da ko wace irin doka, majalisar wakilai, yan siyasa ne, saboda haka babu wani mutum da zai zo ya nade hannun sa ya ce shi ba zai yi siyasa ba.
Amma idan za ka shiga siyasa kasan cewar wace irin siyasa za ka shiga musamman mu da mu ke jagorancin al’umma, ba ka da hurumin da za ka ce a zabi wane ko kada a zabi wane, kowa ya zo ka karbe shi hannu bibiyu, kuma duk Gwamnatin da ta zo ka tsaya ka bata goyon baya tsakani da Allah, domin ya kawo cigaba a Jihar da ka ke, a karamar hukular da

A yanayin kalamanka kamar ka fi karkata a yanzu a bangaren Gwamnati mai ci, gashi kuma ka ce kowa na ka ne, me zaka ce game da haka?
Ai kamar yadda na fada miki dukkan wanda ya ta so ya zo ya nemi mu ba shi shawara za mu ba shi, idan yana neman goyon baya, zamu fada masa hanyoyin da zai bi kuma ko daga wace jama’iyyar ya fito kin ga akan kujerar nan da kika zauna a wannan ofishin a nan Malam Salihu Sagir Takai ya zauna ya nemi goyon baya ya ji matsalolin yan kasuwa, ta ya in ya zama gwamna zai taimaki ‘yan kasuwa ba mu da abin da ya fi wannan kasuwancin, ita wannan siyasa na gaya miki ba yadda za a yi wani ya nade kafa ya ce shi baya siyasa, dole tilas ba a iya gudanar da komai sai da siyasa tun da dukkan mu abin iko yana hannun yan siyasa, to, shi ya sa hatta malaman addini idan ki ka kalla baki sani ba sai dai ki ji an ce malam wane ya shiga siyasa, wani lokacin za ki ga idan wanda ya ke mulki a lokacin ya je masallacin wane ya yi sallah me yiwuwa da akwai sakon da ya ke so ya fada sai ya bayar, a kuma shigar da shi cikin huduba sai ki ji ana cewa malam wane ya shiga siyasa ya bi bayan gwamna, har kullum abin da ya dace mu bi, mu duba, shi, ne; lokaci, komai da lokacin sa.

Mene yake birge ka a cikin wannan siyasar?
To, ni abin da ya fi birgeni, shi ne; in da kullum ake kokarin a taimaki matasa, saboda yanzu ana gani yadda kididdiga ta nuna shi ne, daga nan zuwa shekara ta 2030 Nijeriya za ta zamana tana dauke da mutum miliyan dari biyar da hamsin, yanzu tafiyar da ake mu mutum miliyan dari biyu ne a Najeriya, idan muka zama miliyan dari biyar kusan(a yawa) mu ne na uku a duniya, ba ma a Afirka ba.
Lokacinmu nan ba mu da ita irin wannan ta sun idan suka zo sai su siyi irin kayan mu na nan arewacin Nijeriya su tafi da shi can kudanci, ta haka sai mutanen mu suka fara tasowa nan suna zuwa suna gudanar da harkokin kasuwanci, daga nan sai aka samu kulla mu’amula tsakanin Bahaushe da Igbo da suke cikin wannan kasuwar.
To, shi ne har tafiyar da ake a yanzu yadda kasuwar Sabongari ta bunkasa akwai rumfuna sama da dubu goma sha hudu, tsakanin kananan rumfuna da manyan rumfuna, mutanen da suke shigowa kasuwar nan domin su yi siyayya muna da mutane dai-dai sama da mutum dubu dari biyar wanda a kullum za su shigo su yi siyayya, ita wannan kasuwa ta mu tana da manyan kofofi guda goma sha shida (16) da su ke zagaye da ita ta kowane bangare, ita kuma wannan kasuwar ta yi kusurwane ta bari guda uku, akwai barin gabas, shi ne ake cewa, Igbo Road by Market, akwai barin yamma, inda ake cewa Court Road, wato ‘YanKura Ke nan, akwai kudu, inda ake ce masa France Road, akwai arewa, inda ake ce masa Murtala Muhammad Way, wannan kasuwa haka ta zo ta kasu kuma girmanta sakwaya(skuare) ne, kullum al’umma suna shigo wa daga wurare daban-daban na fadin Afirka, akwai wandan da suke shigowa daga Burkina daga Kamaru daga Afirka ta Tsakiya (Central Africa) daga Ghana daga Chadi.

Ban da kananan hukumomi arba’in da hudu da wadansu jihohin Nijeriya, haka kuma, idan sun gama harkokin kasuwancinsu za su tafi gida su je su kwana, to, ban da su muna da al’umma na jihohi daban-daban da na kasashe su ma za ka ga al’ummar Sin(China)za ki ga na Lebanon da na Pakistan za ka gansu dai iri iri har mutanen Misra (Egypt) domin su gudanar da harkokin kasuwancin su domin su,siya ko su siyar, to, wannan shi ne kadan daga cikin tarihin kasuwar nan.
Saboda haka, wannan kasuwa ta sabongari, kasuwa ce, wadda za ka iya kiranta da kasuwar duniya, domin kuwa daga sassa daban-daban na duniya ake zuwa a saya ko a sayar da kaya a kowace rana.
Wannan shi ne, kuma babban dalilin da ya sa kullum hada-hadar kasuwanci ke kara habaka a wannan kasuwa da ke garin na Kano.

 

Exit mobile version