Sayyadi Ismail Umar Mai Diwani" />

Bai’atur Ridwan: Sahabban Da Suka Yi Mubaya’a Da Manzon Allah Sun Yi Da Allah Ne (I)

A uzu billahi minas shaidanir rajim. Bismillahir rahmanir rahim. Allahuma salli ala Sayyidina Muhammadin Alfatihi lima uglika wal khatimi lima sabaka nasiril hakki bil-hakki wal hadi ila siradikal mustakimi wa ala alihi hakka kadrihi wa mikdarihil azim. Wa radiyallahu an As’habi Rasulullahi (SAW). Wa la haula wa la kuwwata illa billahil aliyyil azim. Ya Himmatas Shaikh ihdiri lana bi hazal mahdari wal ta’adifi bi nazaratin ta’ati lana biz zafari. Za mu cigaba da karatunmu daga inda muka tsaya a makon jiya.

Kamar yadda muka yi bayani a makon da ya gabata, Allah ya sanya Manzon Allah (SAW) a matsayin shugaban ‘ya’yan Adam kaf. Allah ya hada ambatonsa da ambaton Allah. Allah ya sanya yardar Manzon Allah ta zama yardar Allah ce. Allah ya sanya shi a matsayin dayan rukunin Tauhidi, wato in dai ka ce “La ila ha illal lahu” ba ka ce “Muhammadur rasulullahi” ba, Musuluncinka bai tabbata ba. Kafiri idan ya zo shiga Musulunci aka ce ya fadi “La ila ha illal lahu…” ya fada, aka zo “Muhammadur rasulullah” sai ya ce a’a, ai cewa aka yi a kadaita Allah don haka ba sai ya fada ba, idan ya yi haka, shin ya musulunta? Ai Musuluncinsa bai inganta ba.
Sannan bayan duk wannan, a cikin Surar dai ta Fat’hi, Allah Ta’ala ya yi bayani a kan “Bai’atar Ridwani” wato mubaya’ar nan ta yarda (caffa), mubaya’ar nan da Sahabbai suka yi masa a kan babu-ja-da-baya ko dai su shiga Makkah ko kuma su kare. Wanna kissa ce da galibi aka sani ta Hudaibiyya. Lokacin da Manzon Allah (SAW) ya zo Umura da Sahabbansa kafiran Makkah suka tare shi, to an ambace ta da Caffa ta Yarda, saboda Allah ya yarda da dukkan Sahabban da Manzon Allah ya zo tare da su.
Bai’atar Ridawani ta faru a lokacin da Hijira take shekara 6 da yi. Allah Ta’ala ya ambaci bishiyar da abin ya faru a karkashinta, to sai bishiyar ta zama Musulmi suna girmamata kwarai da gaske har zuwa zamanin Sayyidina Umar (RA). Da ya ji tsoron kar wata fitina ta faru da kuma irin ijtihadinsa, sai ya tumbuke ta gabadaya. kila mutum 1,400, kila mutum 1,500 ne suka yi wa Manzon Allah (SAW) mubaya’a a lokacin. Allah ya kiyaye ba a yi yakin ba, aka yi sulhu.
Allah ya ce ai wadanda suka yi Caffa da kai (ya Rasulallah), suna yi ne da Allah, wato da Allah suka yi (mubaya’a) saboda da Annabin Allah suka yi. Ai da Allah (Sahabbai) suka yi mubaya’a a wannan mubaya’ar da suka yi da kai (ya Rusulullah), Hannun Allah (yadda ya dace da shi Subhanahu wa Ta’ala) yana a kan hannunsu lokacin da suka yi mubaya’ar.
kila wasu malamai sun fassara wurin da aka ce “Hannun Allah” ana nufin “karfin Allah” ne. Wasu malamai kuma suka ce kila ana nufin “Ladan Allah” ne saboda duk wadanda suka yi mubaya’ar Allah ya ce ya yarda da su kuma ya ba su lada mai girma. A’a, wasu malaman kuma sun ce ana nufin “Baiwar Allah”, wasu kuma suka ce “kudurta Alkawarin da aka yi” ne. To duka wadannan fassara da aka yi cewa “Hannun Allah” ana nufin “karfin Allah ne ko Lada ko Baiwa ko kudurta Alkawari”, an aro ne, wato majazi ne. Domin duka wadannan da hannu ake yi. Idan za a nuna karfi da hannu ake yi, idan lada za a bayar da hannu ne, haka dai, to aka ce kila shi ya sa Allah ya ambaci “Hannu” a wurin. Haka malamai (na zahiri) suka fassara, amma su malamai rabbaniyyai sun yi zauki sai suka fahimci abin kuma dole sai da zauki da tarbiyya za a fahimci abin. Domin Allah ya ce “Inna” ma’ana “kadai dai”, to in duk ba a gane Nahawun ba, sai Allah ya yi abin dalla-dalla ya ce “Yadullahi” wato “Hannun Allah”. To amma dai sai da zauki. Sannan ko mun gane ko ba mu gane ba, saboda girman Manzon Allah (SAW) za mu sakar masa lafazin don kowa ya san babu wani da aka taba fada wa hakan idan ba Manzon Allah (SAW) ba. Kuma duk da haka, fassarar da malamai suka yi tana nan.
Abin da ake ce wa “majazi” da larabci shi ne “lafazin da aka ciro shi daga ma’anarsa zuwa wata ma’ana da ta saba wa hakikarsa. Ba hakikar abin ake nufi ba, zahiransa ake nufi”. Kamar misali mutum ya ce “na ci abinci na koshi”, to abinci zai iya kosar da mutum? Allah ne yake kosarwa, amma kuma idan mutumin bai ci abincin nan ba zai koshi? Wani karin misali shi ne, mala’ikan mutuwa shi ne mai daukan rai amma kuma majazi ne aka ba shi, Allah Tabaraka wa Ta’ala shi ne hakikanin mai kashewa. Irin wadannan misalai suna nan a cikin maganganun larabawa da yawa, wanda bai da ilimin abin idan an fadi sai ya ce an yi “kafirci” a uzu billahi ko kaza da kaza, duk abin ba haka yake ba.
Wannan lamari na muba’yar da Sahabbai suka yi wa Manzon Allah (SAW), Allah ya ce ba shi suka yi wa ba, Allah ne suka yi wa, yana nuna girman wannan mubaya’ar ne.

Exit mobile version