Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
Home DAUSAYIN MUSULUNCI

Bai’atur Ridwan: Sahabban Da Suka Yi Mubaya’a Da Manzon Allah Sun Yi Da Allah Ne (II)

by Muhammad
February 19, 2021
in DAUSAYIN MUSULUNCI
4 min read
Sahabban
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram

‘Yan’uwa assalamu alaikum wa rahmatullahi ta’ala wa barkatuhu.

Idan ba a manta ba, a makon da ya gabata mun tsaya ne a bayanin da muka yi cewa abin da ake ce wa “majazi” da larabci shi ne “lafazin da aka ciro shi daga ma’anarsa zuwa wata ma’ana da ta saba wa hakikarsa. Ba hakikar abin ake nufi ba, zahiransa ake nufi”. Kamar misali mutum ya ce “na ci abinci na koshi”, to abinci zai iya kosar da mutum? Allah ne yake kosarwa, amma kuma idan mutumin bai ci abincin nan ba zai koshi? Wani karin misali shi ne, mala’ikan mutuwa shi ne mai daukan rai amma kuma majazi ne aka ba shi, Allah Tabaraka wa Ta’ala shi ne hakikanin mai kashewa. Irin wadannan misalai suna nan a cikin maganganun larabawa da yawa, wanda bai da ilimin abin idan an fadi sai ya ce an yi “kafirci” a uzu billahi ko kaza da kaza, duk abin ba haka yake ba.

samndaads

Wannan lamari na muba’yar da Sahabbai suka yi wa Manzon Allah (SAW), Allah ya ce ba shi suka yi wa ba, Allah ne suka yi wa, yana nuna girman wannan mubaya’ar ne.

Akwai irin hakan a wata ayar ta daban ma, inda Allah ya ce “Ba ku kuka kashe su ba, sai dai, Allah ne ya kashe su”. A wata ayar kuma Allah ya ce wa Manzon Allah (SAW), “(a lokacin) da ka yi jifan nan, ba kai ka yi ba, Allah ne ya yi ta”. Ranar yakin Badar Manzon Allah ya debi kasa da tsakuwowi ya watsa wa kafirai, wannan damka daya da ya yi sai da ta cika ido da hancin kafirai dubu (1,000). Ranar yakin Hunaini Manzon Allah (SAW) ya yi irin haka din ma, a nan sai da idon kafirai wajen dubu talatin (30,000) suka cika da kasa. Shi ne Allah Tabaraka wa Ta’ala yake cewa a lokacin da ka yi jifa ba kai ka yi ba Allah ne ya yi.

Yadda maganar take, an san karfin dan adam ba shi da iko sadar da wannan jifar. Domin a ce hannu guda daya ya debi kasa ya yi wannan jifar bai fi ya samu mutum biyar ba, iska ma za ta iya kwashe ta, amma a ce kasar nan ta tafi ba wai ta samu mutum daya ko biyu ko uku ba, a’a har mutum dubu kuma duk ta cika musu ido da hancina a Badar, a Hunaini kuma ta samu mutum dubu talatin duk ta cika musu ido, an san karfin dan adam ba shi da ikon ya yi wannan. Karfin Dan Adam ba shi da ikon sadar da wannan jifar zuwa wurin da aka kai ta har ya zama babu wani daga cikin kafiran nan da kasar ba ta cika idonsa ba (a Hunaini). Ka ga karfin Dan Adam ba zai iya wannan ba, sai dai karfin Allah. To amma shi wannan Dan Adam din (Manzon Allah SAW) Annabin Allah ne, Kalifan Allah ne, ba kamar sauran ‘ya’yan Adam yake ba. Ko da ma a ce karfin nasa ne ya yi amfani da shi, majazi ne, domin shi Annabin Allah ne.

Haka kisan nan ta mala’iku da suka yi wa kafirai a ranar Badar da ranar Hunaini shi ma a hakikarsa yake. An fada a wata ayar kuma cewa ita (ma’anar wannan) tana kan majazin nan, kamantawa ne na Larabawa, haka maganar Larabawa take zuwa, fuskantar lafazi ne da dacewarsa (wadda ake cewa “mushakala”), ma’ana ai ba ku kashe wadannan mutane ba, kai (ya Rasulallah SAW) ba ka jefe su ba lokacin da ka jefi fuskokinsu da tsakwankwani da kasa din nan sai dai Ubangiji ne ya jefi zukatansu da rashin hakuri.

Kuma ma’anar takan zo da wani abu, yanzu dai Annabi (SAW) ya debi wannan kasa ya yi jifa to kuma jifar da cika idon da aka yi sai Ubangiji ya cika zukatansu da tsoro, “(za su yi tunanin) yanzu wannan wani irin mutum ne ya debi dan wani abu kadan ya jefe mu amma duk ya gama da mu?” wannan shi ya ba su tsoro suka watse. Ba ka yi jifa ba yayin da ka yi jifar nan, Allah ne ya yi jifar ta hakika don shi ne ya sa tsoro a zukatansu.Wato Allah ne ya yi natijar jifar. Misali idan mutum ya yi tsawa so yake a ji tsoro a daina wani abu, idan ya kai duka so yake a ji tsoro a yi wani abu, don haka sa wannan tsoron da komai Allah ne ya yi ga kafiran. Ai amfanin wannan jifar da Manzon Allah (SAW) ya yi yana daga cikin aikin Allah, to kuma haka nan shi (Allah Ta’ala) shi ne mai kashewar, shi ne mai jifar don shi ya sa amfanin jifar da kuma amfanin yakin a ciki. Shi kuma Manzon Allah a ma’anar suna ne ya yi jifar. Irin wannan wurin dai a fahimce shi a cikin zauki shi ya fi. Mai littafin nan Alkadi Iyad malami ne Arifi masanin Allah. Yana kawo wadannan ne don a bai wa malaman zahiri hakkinsu, ba don haka ba, girman Manzon Allah (SAW) ya wuce duk a tsaya wannan.

Allah ya taimaki Manzon Allah (SAW) da tsoro, da ya yi niyyar zai je wurin kafirai sai Allah ya jefa musu tsoro su watse.

 

SendShareTweetShare
Previous Post

Yawaitar Hadurra: Gajiya Da Raunin Tunanin Direba

Next Post

Waiwayen Kanun Labaru: Daga Litinin 3 Zuwa Alhamis 6 Ga Rajab 1442 Bayan Hijira  

RelatedPosts

Gudummawar Gwarzon Musulunci Shehu Ibrahim Inyass A Karne Na 20 (1)

Gudummawar Gwarzon Musulunci Shehu Ibrahim Inyass A Karne Na 20 (1)

by Sulaiman Ibrahim
1 day ago
0

Daga Sayydi Ismail Umar Mai Diwani ‘Yan’uwa Musulmi assalamu alaikum...

Bai’atur Ridwan: Sahabban Da Suka Yi Mubaya’a Da Manzon Allah Sun Yi Da Allah Ne (I)

Bai’atur Ridwan: Sahabban Da Suka Yi Mubaya’a Da Manzon Allah Sun Yi Da Allah Ne (I)

by Sulaiman Ibrahim
2 weeks ago
0

A uzu billahi minas shaidanir rajim. Bismillahir rahmanir rahim. Allahuma...

Darajojin Manzon Allah (SAW) Da Suratul Fat’hi Ta Tattare (IB)

by Muhammad
3 weeks ago
0

Allah ya ce wa al’ummar Annabi su girmama shi (SAW),...

Next Post
Labaru

Waiwayen Kanun Labaru: Daga Litinin 3 Zuwa Alhamis 6 Ga Rajab 1442 Bayan Hijira  

Domin sanya talla ko karin bayani a tuntube wannan numbar +2348126152609.

ADVERTISEMENT
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us

© 2020 Leadership Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2020 Leadership Group .

Go to mobile version