Baje Koli: Yadda Aka Kwashe Shanu Daga Tsauni A Jirgi Mai Saukar Ungulu A Suyizalan

Saniya

An yi jigilar wasu shanu a kasar Suyizalan (Switzerland) daga wuraren kiwo na saman tsauni zuwa kasa ta jirgi mai saukar ungulu, a wani bangare na shirye-shiryen bikin baje kolin shanu na shekara-shekara da ake yi a kasar.

Domin taimaka wa dabbobin da suka ji rauni wajen saukowa daga wuraren kiwo na bazara a kan tsaunuka, manoma sun shirya jigilar shanu 10 ta jirgin don a ba su kariya ta musamman zuwa yankin da za su fi samun saukin zirga-zirga.

An kwashe shanun ne daga saman tsauni zuwa kasa a wasu manyan a filayen da ake kira Alpine ta hanyar dabaru na ban mamaki.

Kimanin 10 daga cikin dabbobin an dauke su ta jirgi mai saukar ungulu a cikin wata raga da ake sakalo su daga saman tsaunin zuwa yankin Klausenpass da ke tsakiyar kasar.

An yi ta amfani da kayan damara, domin sauko da shanun ta hanyar sanya wani dogon kebul da ke karkashin jirgin da aka sakale da ragar da za ta dauke su yayin da suke tafiya a sararin Subhana kafin saukarsu zuwa inda aka tanada.

 

Manoma masu jiran ganin an gudanar da aikin, su ma  sun yi amfani da igiyoyi masu karfi don taimaka wa kawo shanun zuwa kasa lafiya, kafin a shigar da su cikin tsarin da ake yi na gwajin bakin.

A halin yanzu, wasu karin dabbobin da suke da karfi sosai sun sake hawa zuwa saman dutsen da kofato. Wani manomi da ake kira Jonas Arnold ya ce: “Dalili daya na safarar jirage masu saukar ungulu don debo wadannan shanu shi ne, ba za ku iya kai wa wasu wuraren da dabbobin ke kiwo da mota ba, daya dalilin kuma shi ne, wasu shanun sun ji rauni, don haka ba lallai ne su iya tafiya daga saman dutsen har zuwa kasa ba.”

Ya kara da cewa: “Ban tambayi saniya yadda take ji yayin da ake dauke ta daga saman tsauni zuwa wancan filin, kamar yadda na san ba za ta iya amsawa ba, amma dai abin da na tabbatar wa da kaina shi ne na san akwai tazara tsakanin saman tsaunin da kasa.” Kuma jirgi ne zai yi aiki wajen dauko su na wani gajeren lokaci.

Ban lura da wani banbanci tsakanin wanda ya tashi sama da wanda ke tafiya a kasa cikin kwanciyar hankali ba. ”

 

Gabadaya, adadin yawan garken shanun ya kai 1,000, don haka kashi daya ne daga ciki kawai aka samu damar ba su taimako na sauko da su kasa. Suna nan zuwa yankin Urnerboden a Switzerland, kuma ana shirin yin faretinsu na shekara -shekara a can.

Exit mobile version