Connect with us

KASASHEN WAJE

BAKIN HAURE: Ma’aikatar Shari’ar Amurka Ta Kalubalanci Hukumcin Kotu

Published

on

Gwamnatin shugaba Trump ta ce, hukumcin da wani alkali ya yanke da ya umaraci gwamnati ta sada iyaye bakin haure da ‘ya’yansu wadanda aka raba a kan iyakar kasar Amurka zai sa a tsare kananan yaran a na lokaci mai tsawo fiye da yadda ake yi a halin yanzu.
Ma’aikatar shari’a ta bayyana a cikin wata takarda da ta shigar a kotu jiya jumma’a cewa, “gwamnati ba zata raba iyalai ba, amma zata tsare su tare a lokacin da ake tantancesu bayan an kamasu suna kokarin keta kan iyaka zuwa Amurka.
Yana yiwuwa a tsare iyalai na tsawon watanni ko ma shekaru sabili da dubban takardun bakin hauren da suke jibge a kotu da ba a samu kai wa garesu ba sabili da yawansu.
Wata dokar kotu da ake kira yarjejeniyar Flore ta hana a tsare kananan yara fiye da kwanaki ishirin.
Alkalin wata kotun Amurka a birnin San Diego na jihar California ya yanke hukumci cewa, tilas ne a gama iyayalan da aka raba cikin kwanaki talatin, a kuma maida kananan yara ga iyensu cikin makonni biyu.
Jami’ai sunce kimanin kananan yara dubu biyu ne suke jira a gamasu da iyayensu
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: