Dakta Sa’idu A. Dukawa
Yau kimanin shekara uku kenan da na gabatar da makala a SAS, Kano, game da matsalar daba a siyasa. Abin da ya afku a hawan daushe na wannan shekara ta 2017, na daba tsakanin magoya bayan ‘yansiyasa biyu, ya nuna bukatar sake tunasarwa game da bukatar kauce wa wannan mummunar dabi’ar. Don haka zan dada lika wannan mukalar.
Kamar yadda wani Bawan Allah ya taba nusarwa, zan raba tunasarwar kashi biyu ko uku saboda sauki ga mai karatu:
Babbar matsala a siyasar Nijeriya ita ce ta daba da amfani da kayan maye da matasa suke yi.
Matasa su ne jigon siyasa a kowace al’umma a tarihin duniya; amman matasan Nijeriya sun sha bamban wajen irin rawar da suke taka wa a siyasar Nijeriya a dalilin daba da ta’ammali da kayan maye da suke yi.
Daba kalma ce da take bayyana wata irin halayya ta matasa wadda ke haifar da sakamako mummuna; daba tana bada hoto na gungun matasa, masu shan kayan maye kamar giya, ko ganyen wi-wi, ko kwaya, ko roche, ko Benylin, ko kashin kadangare, da makamantansu, masu daukar makami, suna farma wadanda ba su ji ba ba su gani ba, ko kuma su farma junansu, ko su farma wanda aka saka su su farmasa.
Idan ‘yandaba suka shiga harkar siyasa, ana kiransu ‘’yanbanga’’; an samu kalmar banga daga kalmar Ingilishi ta banguard, watau ‘yan gaba-dai-gaba-dai!
Ba a taba harkar siyasa ba sai da banguard, watau masu tsayiwar daka, na ko a mutu ko ayi rai sai manufa ta tabbata. Amman idan suka tasirantu da kayan maye, to sun zama ‘yandaba.
Daba A Siyasar Nijeriya
Idan an ci zabe, ‘yanbanga ko ‘yandaba sukan tare a ofisoshin iyayen gidansu don yin maula ta hanyar tare duk wani mai shiga ofis su roke shi kudi; sukan je kafafen yada labarai don yin maganganu na karya da na gaskiya don yabon ubangidansu ko bata abokin hamayyarsa, ko yin raddi ga batancin da aka yi masa, ko tallata shi, da makamantansu su ne, masu kiran kansu sojojin baka, koda yake su sun sha bamban da ‘yandaba; sun fi kusanci da banguard; akan yi amfani da ‘yandaba ma don halaka abokin hamayya; idan suka rasa kudin yin shaye-shaye su kan haura gidajen mutane su yi musu sata, wani sa’in ma har su yi fyade ko kisan kai.
‘Yandaba suna da suna daban-daban: ana kiransu ‘yanjagaliya a Kano da Jigawa, ‘yansara-suka a Bauchi, ‘yan ECOMOG a Borno, ‘yan kalare a Gombe, kauraye a Katsina, area boys a yammacin kasar nan; da makatansu;
Ko ba a fada ba, babu al’ummar da za ta amince da harkar daba a siyasa, ballantana al’ummar Musulmi wacce aka ce mata ‘’kuntum khaira ummatin ukhrijat linnasi…; [ku ne fiyayyun al’umma da aka fitar a bayan kasa: kun kasance kuna umarni da kyakkyawa kuna hani da mummunan aiki, kuma kun yi imani da Allah…]; Kur’an, 3:110.’’
Ko tsarin mulkin Nijeriya ya haramta daba a harkar siyasa a sashe na 227: ‘’[ba a yarda wata kungiya ta mallaki ko ta tanadi ‘yandaba ba, ko ta bada horo ko makami ga wani ba, ko wasu mutane domin yin amfani da su wajen gwada karfi ko tursasawa don neman biyan bukatar siyasa, hasali ma ba a yarda a bar gurbin zato na cewar an tanadi karen bana domin yin maganin zomon bana ba].’’
Matasa Da Harkar Siyasa
Kamar yadda muka fada da farko, siyasa a ko’ina sai da banguard’, wadanda a ko’ina matasa ne.
A kasarar Girka (Greece), wadanda suka haifi tsarin dimokaradiyya, matasa ne wadanda suka jagoranci tafiyar: Socrates da dalibinsa Plato sun jagoranci matasa a kan akidar zuhudu da tsayawa a kan ra’ayi (idealism); su da dalibansu sun yi kokarin cusa wannan ra’ayi a zukatan matasa da tsarin siyasa; suna ganin idan ba an gyara halayyar dan’adam ba babu abin da za a tsinana a siyansance; amman da Aristotle, babban dalibin Plato, da nasa daliban irinsu Thomas Hobbes da John Locke, da J.J. Rousseau da Hegel da Karl Mard sun karkata akalar samari ne wajen fifita abin duniya, ko ra’ayin gina kasa da samar da abinci da kayan alatu a matsayin a’ala a tafikantar da gwamnati da jama’a (materialism). Su suna ganin gina kasa za a yi sai ruhin dan’adam ya gyaru. Wannan ra’ayin shi ya canza siyasar Turai da Amurka zuwa yadda muka santa a yanzu kuma ya shafi tunanin wasu ‘yansiyasar Afirka da Nijeriya.
Masu ilimin falsafa, matasa, Musulmi su suka yi kokarin daidaito da samar da tsakatsakin ra’ayi tsakanin gyaran hali da gina kasa. ‘Yanfalsafa irin su Alkindi da Alfarabi da Alghazali da Ibn Rushd da Ibn Taymiyya, da Ibn Khaldun, da su Abdullahi bn Fodio, duk sun taka rawar gani wajen samar da matsakaicin tunani da ya kamata a tafiyar da tsarin gwamnati. A kurkusa kuma akwai irin su Maududi, da Sayyid Kutub, da makamantansu; duk wadannan suna nuni da cewar duk kokarin gyaran halinka idan ka bar jama’a a cikin talauci za a samu matsala, haka kuma duk kokarin gina kasar ka, idan mutane ba su da ingantacciyar tarbiyya nan ma kana da matsala; shi ya sa muke da bukatar wadanda suke da irin wannan ilimin su karbi ragamar gwamnati su kuma su gwada jagorancin al’umma ko a gane bambancin.
A Afirka tun zuwan Turawan mulkin mallaka, matasa sun yi gwagwarmaya a mataki daban-daban: da Blyden da Senghor sun sa wa matasa kishin al’adun Afirka; da Awolowo da Azikwe sun nemarwa matasa gurbi a gwamnatin ‘yanmulkin mallaka; da Nkurumah, da Fanon, da Cabral, da Sekou Toure sun koyawa matasa turjiya da daukar makami don fatattakar Turawa; da Aminu Kano, da Raji Abdallah, da Sa’adu Zungur sun koyawa matasa ‘’na ki’’! Duk wadannan matasa ne wadanda suka jagoranci wasu matasan!
A siyasar Nijeryia, duk ‘yansiyasar Jamhuriyya ta farko matasa ne: irin su Maitama Sule, su Shehu Shagari, su Muhammadu Ribado, su Augustus Adebayo, su Sam Mbadiwe, wadanda su aka fi jin amonsu a Majalisa; da faduwar jamhuriyyar farko, sojojin da suka karbe ragamar mulki duk matasa ne: irin su Yakubu Gowon, su Muhammadu Buhari, su Sani Bello, su Sani Sami, da sauransu wadanda duk ba su rufa shekara talatin ba kowannansu. A duk misalan da muka bayar babu inda harkar daba ta shiga balle ta yi kamari.
Dakta Sa’idu Dukawa Malami ne a Jami’ar Bayero, da ke Kano, drahmadsaid@yahoo.com
08033225331 (TES Kawai ) ciroma14@yahoo.com