El-Zaharadeen Umar">

Bala Abu Ga Sanata Mandiya: Babu Taimakon Da Ka Yi Wa ‘Yan Gudun Hijirar Faskari

Mataimakin Shugaban jam’iyyar APC yankin Funtua a jihar Katsina, Alhaji Bala Abu Musawa ya bayyana cewa Sanata mai wakilitar yankin Funtua, Sanata Bello Mandiya ya yi watsi da ‘yan gudun Hijirar da ke Faskari suna neman gudunmawa.

Bala Abu Musawa yana wannan magana ne a dai dai lokacin da ‘yan gudun Hijira mutun 3,700 wanda yawaicin su mata ne da kananan yara ke neman taimako a wata firamari da ke Faskari

Rahotanni sun bayyana irin gudunmawar da gwamnatin jihar Katsina da kuma shuwagabanin kananan hukumomin da ‘yan siyasa da masu hannu da shuni suka bada domin tallafawa waxannan baynin Allah su samun saukin rayuwa

Sai dai mataimakin shugaban jam’iyyar na cewa ya kamata Sanata Mandiya ya dawo ya san halin da mutanen shi ke ciki, ya kuma tausaya masu da taimaka masu kamar yadda wanda ya gada Sanata Abu Ibrahim ke yi lokacin da yake rike da wannan matsayin.

Alhaji Bala Abu Musawa ya kara da cewa shi dai a iyakar saninsa da kuma ofis din shi baya da wata masaniya, game da wani taimakon da Sanata Bello Mandoya ya badako ya aiko wani, ya ce haryanzu babu wani sako da ya sameshi balanta a rabawa mabukata da ke wannan sansani na ‘yan gudun Hijira da ke Faskari

Kazalika mutanen yankin Funtua sun bayyana takaicinsu tare da nadamar zaben da suka yi wa Sanata Bello Mandiya a shiyyar Funtua, wanda bincike ya tabbatar da cewa babu wani tallafi ko Jaje balanta na gudummuwa daga Sanata Bello Mandiya

Mazauna wajen sun bayyana yadda masu rike da mukaman siyasa na yankin ke taimaka masu, misali Alhaji Bashir Ruwan Godiya mai ba gwamnan Katsina shawara akan harkar ilmi mai zurfi da kwamishinnan muhalli da dan majalisar jiha mai wakiltar su dama uwa uba gwamnan na Katsina duk suna tallafawa halin da suke ciki.

Sai dai duk da wannan korafi na mutanen wannan yankin, yasa an tuntubi Sanata Bello Mandiya domin jin ba’asin sa gane da wannan korafi ta hanyar buga waya da aika sakon kar ta kwana a wayarsa, don jin ta bakinsa, sai dai kash ba a samu nasarar hakan ba. Haka kuma mun yi kokarin jin ko yana da masu tafiyar da harkokinsa shima shiru kaki ji kamar an tura Bello Mandiya Sanatan Yankin Funtua

Exit mobile version