Connect with us

LABARAI

Bal’a’in Rusau: An Damfari Gwamnan Bauchi –Wadanda Abin Ya Shafa

Published

on

Dubban mutanen da su ka gamu da ta’adin iska da ruwa mai karfi su ka rusa ko lalata gidajensu sama da 10,000 a ciki da wajen garin Bauchi sun bayyana zargin cewa, jami’an da gwamnan jihar ta tura domin su kai mu su taimako sun damfari gwamnan jihar ta hanyar kin isar da sakon yadda ya kamata. Don haka wadanda abin ya shafa su ka koka game da karancin kulawa ko bayar da taimako daga gwamnatin jihar Bauchi, inda wasu daga cikin irin wadannan mutane su ka ziyarci cibiyar ’yan jaridu ta Bauchi su ka koka da cewa tun daga lokacin da wannan matsala ta afka mu su mako biyu har zuwa wannan lokaci babu wanda ya kawo mu su ziyara ko ya nuna mu su tausayawa da nufin a faranta mu su rai ko ba su tallafi daga gwamnatin jihar Bauchi da nufin rage mu su radadin bala’in da ya same su, inda su ka bayyana korafinsu game da yadda su ka ji Gwamna Mohammed Abdullahi Abubakar na jihar ta Bauchi ya shiga kafafen labarai ya na bayyana cewa ya bayar da tallafi, alhali babu wanda ya ziyarce su ko ya ba su wani abu, a cewarsu.
Cikin mutanen da su ka ziyarci wakilinmu akwai Malam Mahmud Musa Ustaz Mainama da ke kasuwar Wunti. Ya koka game da karancin taimakon da a ka yi ma sa, saboda dakuna uku da bangon gidansa duk sun rushe yadda a halin yanzu ya ke fakewa a wata makaranta da ke makwabtaka da ita. Ya bayyana cewa, akwai kaskanci cikin lamarin yadda a ka ba shi rabin mudun masara a matsayin tallafi daga gwamnatin jihar Bauchi, inda ya bayyana cewa ya yi asara mai tarin yawa, amma an ba shi wani tallafi kamar wasan yara daga gwamnatin jihar.
Mahmud Musa ya bayyana cewa, a unguwarsu da ke Mangwarojin Angasawa cikin garin Bauchi sama da mutane 50 kowa an ba shi mudu guda ko rabin mudu, inda ya bayyana cewa a matsayinsa na magidanci mai mata guda da yara takwas wannan tallafi abin kaico ne ga wannan gwamnati ya kamata su rika daukar lamurran mutane talakawa da muhimmanci idan kuma ba za su tallafa ba su bari kawai shi ne ya fi alheri, domin bata sunan gwamnati ne. Ya kara da cewa, a gwamnatocin baya ba haka a ke bayar da taimako ba; a na yi ne tare da nuna karimci da tausayawa wajen bayar da taimako ba nuna izza da isa ko karya da yaudara ba.
Don haka ya kara da bayyana cewa, a halin yanzu ya na zaune a ajin wata makaranta ce da ke kusa da gidansa, ne, saboda ba shi da kudin da zai kama haya kuma ba inda zai kai kukansa. Don haka ya nemi gwamnati da ta agaza ma sa ta taimaka. Ya ce, idan kuma gwamnati ba za ta iya ba, masu hannu da shuni su taimaka mu su da tallafi na gaskiya. Kuma ya bayar da shawarar duk wani tallafi da kungiyoyi da masu hannu da shuni za su bayar kar su ba jami’an gwamnati, su raba kai tsaye ga wadanda wannan matsala ta rutsa da su shi ne mafi alheri, saboda idan an bayar sakon ba ya isa kamar yadda ya dace.
Shi ma wani magidanci da ke unguwar Kandahar mai suna Malam Mohammed Sabo ya bayyana cewa tun da wannan abu ya rutsa da su a na neman mako biyu kenan babu wanda ya zo ya tambaye su irin matsalar da ta same su da nufin zai taimake su illa kurum su na jin gwamnati na watsawa a kafafen rediyo da talabijin cewa ta bayar da taimako alhali su ba abin da su ka gani. Don haka ya bayyana cewa, wannan gwamnati ta na daukar shugabancin kamar wasa, inda a kullum duk abin da su ke fada a baki ne kurum babu cikawa, alhali mutane sun kawo su ne da nufin za su yi mu su adalci don ciyar da rayuwarsu gaba, amma abin ya zamo yaudara da ci da addini ko ci da ceto.
Mazauna unguwar Gawo da ke Inkil sama da mutane dari wannan matsala ta shafa inda gidaje kusan 20 su ka rushe, amma har yau su ma sun bayyana cewa babu wanda ya zaga ta kansu, don yi mu su jaje ko kuma bayyana alhininsa game da abubuwan da su ka faru, yayin da wasu kuma da ke kusa da su a ka bayar da buhu biyu na shinkafa da masara, don a raba mu su yadda wasu su ka samu mudu biyu wasu kuma su ka samu mudu uku a gidajensu kowanne, musamman ganin akwai Malam Mohammed Sani wanda ya jima shekaru biyar ya na gina daki biyu kuma cikin wahala ya ke tafiya kwadago ya samo kudi har ya kai ga rufa gidan, amma lokaci daya iskar ta rusa dukkan gidan ba abin da ya saura kuma a halin da ake ciki yanzu iyalansa sun koma gidan iyayen matarsa don ba yadda zai yi.
A unguwar Turum ’yan sarki iskar ta yi barna sosai yadda wani magidanci Idris Abdullahi ya bayyana cewa tun lokacin da wannan masifa ta fada garin na Bauchi sama da mutane goma gini ya kwanta kansu a unguwar kuma duk sun mutu, amma har zuwa wannan lokaci ba wanda ya zo daga gwamnati ya basu tallafi ko jajanta musu. Illa sun ji wucewar gwamna da Sarkin Bauchi zuwa fadar sarkin Turum yadda shima ya gamu da wannan barna ta iska don haka can gwamnan da sarkin Bauchi suka ziyarta amma ba su ziyarci talakawa ba a garin na Bauchi. Amma daga baya mun samu labarin suma an kai taimako gidaje inda aka raba mudu biyar na masara ko shinkafa ko garin kwaki a kowane gida da wannan matsala ta auku.
Wakilinmu wanda ya zaga sassa daban-daban na garin Bauchi don ganewa idon sa halin da mutane ke ciki ya zuwa wannan lokaci mutane na cikin mawuyacin hali inda su ke fadin munanan kalamai wa gwamnati mai ci saboda rashin bayar da wani tallafi ga mutanen da wannan wakika ta abka musu yadda hatta ziyarar da gwamna Mohammed Abdullahi Abubakar da Sarkin Bauchi Rilwanu Sulaimanu Adamu su ka fita, don duba yadda su ka ga barna akasari sun je gine-ginen gwamnati ne yadda a ke ganin gwamnan zai iya samun tallafin gwamnatin tarayya don gyara wuraren inda ake ganin za a yi cuwa-cuwar kwangilolin gyaran gine-ginen gwamnati ne kurum.
Cikin wannan mako ne gwamna Mohammed Abdullahi Abubakar na Jihar Bauchi ya sanar da kafa kwamiti mai mutane biyar da nufin su zaga garin Bauchi domin duba gidaje sama da dubu goma da wannan ta’adi ya shafa masu manya da kananan matsaloli. Lamarin da ake ganin ko mutane talatin ne cikin kwamitin idan sun raba kansu gida shida za su kwashe kusan mako guda kafin su zaga cikin da wajen garin Bauchi kurum kafin a ce sun fita wajen garin Bauchi da nufin lissafa gidajen da wannan matsala ta shafa. Don haka ake ganin har yanzu gwamnatin Jihar ta Bauchi babu wani nau’i na tausayi cikin zukatan su yadda tun daga wancan lokaci gwamna Mohammed Abdullahi Abubakar ya shiga kafafen labarai na kasa da kasa yana neman tallafi, kuma akwai mutanen da sun kawo iya gwargwado wanda ake zaton shi ne kurum gwamnatin ta raba wa masu rabo da suka samu rabin mudun masara ko gero ko garin kwaki zuwa mudu uku.
Don haka a ke ganin har yanzu akwai matsala game da mawuyacin halin da mutane suka shiga ba kamar yadda aka saba a gwamnatocin baya ba, yadda idan wani abu ya faru na matsala kwana uku ya yi yawa kowa ya samu tallafin gwamnati, amma zuwa wannan lokaci babu wani abu na a zo a gani da ya shiga hannun mutane. Bilhasali sama da rabin mutanen da abin ya shafa ba wanda ya taka unguwannin su da nufin jajanta musu ko basu tallafi komai karancin sa. Don haka akwai aiki mai girma a gaban wannan gwamnati da a kullum damuwarta shi ne yadda za ta tara kudi da kuma yadda za ta nemi kudi daga hannun kamfanoni ko mutane amma ba a sanin hanyoyin da ake bi domin kashe kudin ta yadda zai amfani mutanen Jihar Bauchi.
Cikin wadanda suka kawo tallafi Jihar ta Bauchi akwai tsohon mataimakin shugaban kasa Alhaji Atiku Abubakar da Gwamnan Jihar Gombe Alhaji Ibrahim Hassan Dankwambo yadda kowannen su ya bayar da taimako naira milyan goma goma a Bauchi haka kuma suka bayar da naira milyan goma goma a garin Azare inda suka gama da ibtila’in gobara a kasuwar garin. Yayin da kuma suka kara da tirelolin shinkafa da masara da man girki da sauran su. Bayan haka kuma akwai wasu da dama da suka bayar da tallafi amma har zuwa wannan lokaci mutane basu ji irin tallafin da shugaban kasa ko gwamnatin Jihar Bauchi suka bayar na kashin kan su ba don rabawa mutanen da matsalar ta shafa.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: