Dan wasan kasar Wales, Gareth Bale, ya buga wa Real Madrid wasanni na 250 a karawar da kungiyar ta doke kungiyar kwallon kafa ta Eibar da ci 3-1 ranar Lahadi a gasar La Liga wasan mako na 28 a wasan farko na komawa gasar.
Dan wasan tawagar Wales wanda ke buga kakar wasa ta bakwai a Real Madrid an ci wasanni 162 da shi ya kuma ci wa kungiyar kwallo 105 tun bayan komawarsa kungiyar daga Tottenham a shekara ta 2013.
Cikin wasanni 250 da ya yi wa Real Madrid ya buga wasannin La Liga 170 a gasar cin kofin zakaratun turai ta Champions League 55 da Copa del Rey 13 da kofin zakarun nahiyoyin duniya wato Club World Cup wasanni 6 da Spanish Super karawa uku da kuma European Super Cup wasa uku, sannan ya buga fafatawa 19 a kakar bana.
Kakar wasan da Bale ya fi buga wa Real Madrid wasa ita ce ta shekarar 2014 zuwa 2015 wadda ya yi wasanni 48 wasannin da ya fi buga wa shi ne na hamayya sau 20, kuma kungiyar da ya fi zurawa kwallo a raga ita ce Real Sociedad har karo tara.
Cikin kwallo 105 da ya ci sun hada da 80 a La Liga da 16 a kofin zakarun turai na Champions League da kwallo 6 a Club World Cup da kuma 3 a Copa del Rey duka a zamansa na Real Madrid.
Wasannin da ya fi bajinta sun hada da kwallo hudu da ya zura a ragar Rayo Ballecano a kakar 2015 zuwa 2016 da kuma uku rigis da ya ci Balladolid a kakar 2013 zuwa 2014 da Deportibo de La Coruna a kakar wasa ta 2015 zuwa 2016 da kuma Kashima Antlers a kakar wasa ta 2018 zuwa 2019.
Bale ya kuma ci wa Madrid kwallayen raba gardama a fafatawa uku da zumullar kwallo hudu a raga kuma a wasan karshe sannan shi ne ya ci biyu a Champions League da Real Madrid ta doke Liberpool ya kuma ci San Lorenzo a Club World Cup a 2014 zuwa 2015 da kuma wadda ya zura a ragar Barcelona a Copa del Rey a kakar wasan shekara ta 2013 zuwa 2014.