Abba Ibrahim Wada" />

Bale Zai Taimaka Wa Tottenham Wajen Lashe Firimiya, Cewar Modric

Bale

Tsohon dan wasan Tottenham kuma dan wasan Real Madrid wanda suka buga Tottenham da Real Madrid a tare, Luca Modric, ya bayyana cewa Gareth Bale zai taimakawa Tottenham wajen lashe gasar firmiyar Ingila.

Shima dai Gareth Bale, wanda a kwanakin baya ya koma kungiyar a matsayin aro daga kungiyar Real Madrid ya bayyana cewa ya koma tsohuwar kungiyar tasa ne domin ci gaba da kafa tarihi a duniya.
Tuni dai dan wasan ya kammala komawa kungiyar ta birnin Landan bayan da kungiyoyin biyu suka cimma yarjejeniyar kulla yarjejeniya akan kaftin din na tawagar ‘yan wasan kasar Wales wanda a halin yanzu yake fama da ciwo
Kociyan kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid, Zinedine Zidane ne ya nuna yana so a gaggauta sayar da dan wasan wanda kungiyar ta saya da tsada daga Tottenham saboda baya bukatar zamansa a kungiyar kuma bayan Bale yabar Real Madrid Zidane ya bayyana cewa yana farin ciki da abinda ya faru.
Dangantaka tsakanin mutanen biyu, Zidane da Bale ta yi tsami fiye da kima, inda har ta ruguje, har ma ya kasance kungiyar ba ta da wani zabi illa ta sayar da dan wasan saboda baya buga wasa kuma baya tafiya tare da tawagar kungiyar idan zasu tafi wasa bugu da kari yana karbar albashi mai yawa duk da baya buga wasa.
”Bale babban dan wasa ne kowa yasan haka a duniya kuma ya lashe kofuna da dama a rayuwarsa saboda haka yana da kwarewa ta cin kofi hakan yasa nake ganin zai taimakawa Tottenham wajen lashe kofin firimiyar bana” in ji Modric
A ranar daya ga Satumba, 2013, ne Bale ya baro Tottenham zuwa Real Madrid a kan kudin da aka yi amannar ya kai Yuro miliyan 91 kuma ya lashe kofuna da dama a kungiyar ciki har da kofin zakarun turai guda hudu.

Exit mobile version