Abba Ibrahim Wada" />

Balotelli Ya Koma Marseille Da Taka Leda

Dan wasan gaba dan kasar Italiya, Mario Balotelli ya koma kungiyar kwallon kafa ta Marseille da buga wasa kan yarjejeniyar zuwa karshen kakar bana, bayan da ya bar kungiyarsa ta Nice a Faransan.
Dan wasan dan asalin kasar Italiya ya so ya bar Nice tun kafin fara kakar bana, daga baya ya tsawaita zamansa, bayan da ya kasa samun wata kungiyar da zai koma buga kwallo a bara musamman a kasar Ingila.
Balotelli mai shekara 28 a duniya, bai ci kwallo ba a wasanni 10 a kwanan nan, wanda Nice a ranar Laraba ta soke kwantiragin da ta kulla da shi hakan yasa yakoma Marseille domin karasa kakar wasa ta bana.
Nice ce ta sanar da raba gari da ta yi da Mario Balotelli a shafinta na Intanet, inda ta gode masa kan gudunmawar da ya bai wa kungiyar a kaka biyu da rabi da ya yi yana wakiltar kungiyar a wasanni daba daban.
Tsohon dan wasan Inter Milan da Manchester City ya yi suna wajen zura kwallaye a raga a gasar Faransa, tun bayan da ya bar Liberpool zuwa Nice a 2016 sannan ya wakilci kasar Italiya a wasanni daban daban.
Balotelli ya ci kwallo 43 jumulla a zaman da ya yi a Nice, a bara guda 25 ya zura a raga a wasanni 36 da ya yi, hakan ya sa tawagar kwallon kafar Italiya ta gayyace shi a watan Mayun shekarar data wuce.

Exit mobile version