Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
Home MANYAN LABARAI

Bambancin Mai Wasa Da Maciji Da Mai Kama Maciji -Rahama Ubale

by Tayo Adelaja
September 14, 2017
in MANYAN LABARAI, TATTAUNAWA
6 min read
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram

Ga mace mai kamar maza wadda ta shahara a cikin mata ‘yan’uwanta a kan riko da sana’ar mahaifinta na sarrafa macizai yadda ta ga dama. Ba wata ba ce face Rahama Ubale mai macizai Zariya. Wakilinmu Idris Umar Zariya ya zanta da ita a kan yadda take samun wasu sirrori a mu’amulanta da macizai ga yadda a ta su ta kasance.

TAMBAYA: Malama ko za ki iya gaya mana sunanki da alakarki da macizai?

samndaads

RAHAMA: Eh sunana Rahama Ubale mai Macizai Zariya, kuma ni ‘yar asalina jihar Kaduna ce, kuma Bazazzagiya ce ni, duk da yake ruwa biyu ce ni ubana dan Zariya ne uwata kuma ‘yar jihar Kogi ce, na yi karatun firamare na Nyaya Abuja kuma na yi sakandire na a G.G.S.S Samaru yanzu haka ina hanyar shiga jama’a ne.

TAMBAYA: To ko za ki gaya mana yadda kika sami kanki tsundum cikin harkar sana’ar mu’amula da macizai duk da ga shi kina a matsayin ‘ya mace?

TAMBAYA: Kamar ya ? Kin ce tun kina ‘yar kwana daya a duniya.

RAHAMA: Abin da nike nufi a nan shi ne, ka san Bahaushe na cewa, kowane tsuntsu kukan gidansu yake yi. To bias ga al’adar gidanmu duk yaraon da aka Haifa to yana fadowa daga cikin mahaifiyarsa to za a kawo maciji a saka shi cikin kwaryar da za a yi masa wanka da ita ma ana tare za a yi masu wanka da macijin. To, ni ma haka akai min.

TAMBAYA: To Rahama me wannan ke sawa, ko in ce maganin mene ne yin hakan?

RAHAMA: To ka san an ce taskira asirin mai daki, amma a gaskiya hakan wani lakani ne da muka gada iyaye da kakanni kuma daga cikin sirrin shi ne, akwai wani ruwa da shi macijin yake fitarwa daga bakinsa to akwai dafi a cikinsa to a lokacin da ake wannan wankan za ai ta husata macijin don samun wannan ruwan dafin daga bakinsa don a rika shafa wa shi yaron a kansa da bayansa da dukkanin gabobinsa wanda ga irin namu hasashen yana maganin shi kansa cizon macijin da kuma wasu abubuwa da yake sirri ne da ba zai yiwu in sanar da su a nan ba.

TAMBAYA: To yanzu wane sakamako kike samu a mu’amularki da macizai?

RAHAMA: Gaskiya abubuwan suna da yawa. Na farko dai ina bayar da magani idan maciji ya yi cizo kuma akan ba ni kudi masu yawa a matsayin lada. Na biyu duk inda maciji ya shiga in mahaifina ba ya nan don ka san duk fadin Afirka ta Yamma mahaifina ne gagarau a fannin harkar macizai hagu da dama. To komin runtsi zan shirya in je in damko sa. Na uku kasantuwata da macizai nakan fahimci wasu asararu da nake amfani dasu wajan magance wasu matsaloli da suka shafi cituttuka na zamani, ga shi nakan yi wa ’yan makaranta bayani a kan yadda rayuwar maciji take ga masu karanta fannin kimiyar dabbobi a kananan makarantu da Jami’o’i da dai sauransu.

TAMBAYA: Ko kina da miji?

TAMBAYA: To Rahama shin mene ne banbancin sana’arki da kuma sana’ar wasa da maciji da ake yi a kasuwa?

RAHAMA: Gaskiya akwai bambanci mai yawan gaske. Bambanci na farko shi ne, mu gidanmu kama maciji muke yi ba wasa muke yi da shi ba. Kama shi muke yi in ya gagara ko yana kuntata wa jama’a. Sai na biyu mu mukan karance shi ne don amfanar mutane. Sai na uku mu duk macijin da ka gani a wajana to da hakoransa garau ba ma cire masa hakori don mukan dibi dafinsa don yin nazari a kan sada wasu bukatu. Karshe ba ma alfahari da sirrin da Allah ya ba mu a kan maciji sabanin masu wasa da shi ka ga su suka je kasuwa su tara mutane su fito da macizai suna kida ganga suna rantsuwa suna ba da magani ana ba su kudi wanda mu ba haka muke ba .

TAMBAYA: Maciji ya taba cizon ki ko wani naki?

RAHAMA: Wuu ka ji inda muka bambanta da sauran masu kama maciji. Mu gaskiya maciji na cizommu amma Allah ya ba mu wata baiwa da ko ya cije mu to dafin bai shiga cikin jininmu wanda su kuma masu wasa da maciji suna da lakani ne na rufe mai baki yadda bai iya bude bakinsa ballanta har ya yi cizon amma duk randa Allah ya ba shi ikon budewa to sai kaji an ce ya yi can maciji ya ciji wani mai wasa da shi Allah ya kare mu baki daya.

TAMBAYA: To za ki iya gaya mana irin macizan da kike iya kamawa?

RAHAMA: To in kana bibiyar tarihi ko in ce labaru to za ka ji bayani a kan harka  ta kama macizai ko mu ce a duniyar masu kama macizai a gaskita babumacijin da zai gagare ni kamawa komin girmansa kuma duk fadansa kuma duk tsufansa wannan nufin Allah ne don babu wanda bai san mu ba a duniya baki daya in dai a harkan kama maciji ne sai dai Allah.

TAMBAYA: Yanzu haka akwai macijin da kika fi so kuma ya fi burge ki?

RAHAMA: Macijin da na fi so a rayuwata wanda ko barci zan yi sai na kawo shi kusa da ni, ita ce Tandara. Ita ce ba ta fada amma ka ga Kasa da baki da jan nasuri irin su kububuwa da gajera ko masheka ko marda ko kwakiya ga darmansu ba su da kyen kiwo domin sun cika hushi amma in kana son macijin da za ka iya yin kiwon sa to sai Tandara don in ta ji dadin hannunka za ka ga har kyalli take yi, yanzu haka ina siyar da irinta ga masu sha’awar kiwo don sukan yi kwai har su kyankyashe ka san maciji daya yakan kyankyashe kwai dari kuma ga shi ba sa da wabi kokai ai ka san cewa maciji da kada mai shiga ruwa da kunkuru sun fi komi dadewa a duniya. In ba ka sani ba, to na ba ka wannan sirrin.

TAMBAYA: Na ji an ce akwai macijin da ba shi da dafi shin gaskiya ne ko karyace?

RAHAMA: Gaskiya wannan Magana ba haka take ba, gaskiyar maganar shi ne, duk suna da dafi amma wani macijin ya fi wani dafi don in wani macijin ya cije ka to sai ka dauki wani lokaci kafin dafin zai fara cutar da kai, amma wani macijin yana ciro kan dafin zai fara aiki a jikinka wani ma sai ya kai shekara zai fara cutar da kai. Misali kamar Kasa ita farat daya take kashe mutum amma ka ga marda ko sai ka shekara da dafinsa a jikinka kana yawo bai maka komi ba kuma inda zai ciji saniya take za ta mutu.

TAMBAYA: An ce wai macijiyar nan mai suna kasa tana barci. Har ana ce mata sarkin barci shin ya gaskiyar maganar take a gare ki?

RAHAMA: Kirana ga gwamnati ta kirkiro cibiyar hada maganin cizon maciji a dukfadin kasar nan hakan zai taimaka wa jama’a tare da rage rasa rayukan da ake yi a bias ga cizon maciji duk da cewa wanda yake Kaduna bai san cizon maciji ba, amma mutumin Kaltungo ko Jos ko Billiri ya san cizon maciji.

SendShareTweetShare
Previous Post

Fulanin Filato Sun Nisanta Kansu Daga Harin Ancha

Next Post

Barazanar Ambaliya A Jihohi Takwas: NEMA Ta Ce A Kwashe Mutane

RelatedPosts

Gadon Siyasa Da Kasuwanci Na Yi – Hon. Mai-Shanu

Gadon Siyasa Da Kasuwanci Na Yi – Hon. Mai-Shanu

by Sulaiman Ibrahim
5 days ago
0

HON. MUHAMMAD UBA GURJIYA MAI SHANU shine wakilin al'ummar karamar...

Bude Makarantu

Korona: Ba Ja Baya Ga Bude Makarantu – Gwamnatin Bauchi

by Muhammad
6 days ago
0

Daga Khalid Idris Doya, Ma’aikatar Ilimi ta Jihar Bauchi ta...

Harshen Hausa

Taron ‘Waiwaye Adon Tafiya’: Masana Sun Damu Bisa Nakasta Harshen Hausa

by Muhammad
7 days ago
0

Akwai Damuwa Kan Yadda Zamani Ke Tafiya Da Al’adun Bahaushe...

Next Post

Barazanar Ambaliya A Jihohi Takwas: NEMA Ta Ce A Kwashe Mutane

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Domin sanya talla ko karin bayani a tuntube wannan numbar +2348126152609.

Leadership Epaper
ADVERTISEMENT
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us

© 2020 Leadership Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2020 Leadership Group .

Go to mobile version