Nasir S Gwangwazo" />

Bambancin Marubuci Da Jarumi Tamkar Bambancin Sama Da kasa Ne – Gidan Dabino

MALAM ADO AHMAD GIDAN DABINO, MON, mutum ne fasihi kuma jajirtacce a kan dukkan abinda ya saka a gaba. Da yawan masu lura da al’amuran adabi su na kallon sa a matsayin marubuci mafi cimma nasara a tarihin Adabin Kasuwar Kano. A baya-bayan ya tsunduma gadan-gadan wajen fitowa cikin finafinai a matsayin jarumi. Ya fito a finafinan da ba su wuce guda uku ba, amma wani abin dubawa shi ne tuni har ya cimma nasarorin da jarumai da dama su kan kare rayuwarsu ba su taba cimma ba, wato inda Gidan Dabino ya lashe kyautukan yabo a matsayin fitaccen jarumi, ciki kuwa har da samun fitowa a jerin zakakurin jarumin Afrika na Gasar Zuma na shekara.
imma ba. Tun a fim dinsa na farko bayan ya dawo fitiwa a finafinai, wato Juyin Sarauta, jarumin ya mamaye duk wata gasa da a ka gudanar. A yanzu haka kuma ya fara fitowa a cikin wani shirin gidan talabijin na Arewa 24 mai suna Kwana Casa’in, wanda mai dogon zango ne (series). Tun fim din bai yi nisa ba har Gidan Dabino ya fara samun yabo daga masu kallo. Editan LEADERSHIP A YAU, NASIR S. GWANGWAZO, ya samu amsar wasu tambayoyi daga marubucin, wanda ya zama cikakken jarumi, amma a matsayinsa na jarumin ba marubuci ba. Ga yadda tattaunawar ta kasance:

Wannan wata nasara ce wacce hatta manyan jaruman da su ka yi fice sosai da damansu ba su taba.
Shin ka dade da fara fitowa a matsayin jarumin fim?
Na fara fitowa a matsayin jarumi a cikin fim dina na farko mai suna In Da So Da Kauna, wanda mu ka yi a shekarar 1994 zuwa 1996. Lokacin harkar fim ma ba ta kafu sosai ba. Amma harkar wasan kwaikwayo na soma tun shekarar 1984 a kungiyar Gyaranya Drama.

A ganinka, me ya sa ka fi yin shuhura a matsayin marubuci maimakon jarumi?
Harkar rubuce-rubuce na fi yi fiye da ta finafinai, domin rubutu da wallafa shi na fara yi a shekarar 1984, sannan na buga littafin In Da So Da Kauna a shekarar 1990 sai da ya shekara hudu a kasuwa, sannan na fara suna a harkar rubutu shi ne na shirya fim din littafin. Don haka a ka fi sani na a fagen rubutu. Kuma a lokacin littattafai ne su ke tashe ba finafinai ba. A dunkule kuma mu na iya cewa komai da lokacinsa da kuma lokacin da Allah ya ke kawo shi.

Za ka iya ba mu labarin yadda a ka yi ka dawo fitowa a finafinai gadan-gadan?
To, ai ba ni na dawo da kaina ba, dawo da ni a ka yi da karfi da yaji. A cikin shekarar 2017, lokacin da Hajiya Balaraba Ramat Yakub za ta shiriya fim din Juyin Sarauta ta dauke ni a matsayin daya daga cikin masu shiryawa, wato ni da ita ne masu shiryawar (producers). Bayan mun je garin danhassan wajen daukar wasan, jarumin da a ka bai wa matsayin Sarki Yusufa sai ya kasa yi, shi ne a ka tsaya carko-carko. A lokacin ma ni da Bashir Mudi Yakasai ba ma nan garin danhassan mun tafi karamar hukumar Kura wajen jami’an tsaro, don sanar da su kafin mu dawo garin danhassan wajen daukar shirin. Tun kafin mun dawo a ka kira ni a ka ba ni mummunan labarin cewa wanda a ka saka a matsayin Sarki Yusufa ya kasa, ba zai iya ba.
A lokacin ita Balaraba Ramat ba ta zo wajen daukar shirin ba (wato ranar farko), don haka mu ka dawo danhassan, na zo na ga yadda a ke ta karanta wa wannan bawan Allah labarin, amma ba ya iya rikewa. Daraktan fim din Falalu dorayi ya fito ya ce shi fa ya na ba da shawara a sauya wannan jarumin, domin idan ba haka ba sai an yi wata guda a nan garin ba a gama fim din ba.

Na karbi labarin na shiga dakin, na zauna gaban mutumin nan, na karanto ma sa, na yi ma sa bayanin yadda zai yi don ya dinga kawo kalaman da a ka karanta ma sa, sama da minti talatin amma abin ya gagara, dole na hakura ni ma na fito. Aiki dai ya tsaya cak, ko fitowa daya ba a dauka ba, ga rana ta yi, a ka fara tunanin wa za a sanya a madadinsa. Na ce a nemo wani cikin jaruman da mu ke da su a sanya wani. Nan dai a ka ce idan a ka tafi neman wani (mafi yawa duk jaruman sun fita aiki), yaushe za a ci gaba? Sai dai a tashi daga aikin sai an samo wani jarumin.
A nan dai Falalu da Muhammad Reza Shah da Bashir Mudi Yakasai su ka ce ni na fito mana a matsayin Sarki Yusufa. Na ce a a, ai ba zai yiwu ba, Ina matsayin mai shiryawa, kuma na karbi matsayin jarumi, wanda zai fito sama da sau 40 a cikin fim din, abin ya yi min yawa. Da me zan ji? Aikin mai shiryawa ko jarumi? A dai nemo wani. Su ka yi su ka yi, na ce a a. Ban sani ba ashe sun kira Balaraba Ramat sun gaya ma ta abin da ake ciki, sai kawai na ji kiran ta ya shigo wayata. Ina dauka sai na ji ta ce, Adamu don Allah don Annabi Muhammad (SAW) ka daure ka fito a matsayin Sarki Yusufa. Na yi shiru, ta sake yi min magiya. Na ce shi kenan.
To wannan shi ne abin da ya dawo da ni fitowa a matsayin jarumi a cikin shekarar 2017. Daga nan sai kuma na fito a cikin fim mai dogon zango (series) mai suna Bilkisu na kamfanin Amara a matsayin shugaban karamar hukuma a shekarar 2017. Haka nan kuma a cikin shekara ta 2018 na sake fitowa a wani fim din mai dogon zango (series) mai suna Kwana Casa’in na Arewa 24, wanda na fito a matsayin Malam Adamu dan takarar gwamna a jam’iyyar adawa ta Haske Party wanda na ke karawa da Gwamna mai ci, Bawa Mai Kada.

Mene ne dalilin da ya sa a yanzu ka fi karbuwa a matsayin jarumi?
To, ba zan iya cewa ga dalili ba sai dai ko a yi hasashe. A na iya cewa da man can sau daya na taba fitowa a matsayin jarumi a cikin fim din In Da So Da Kauna a shekarar 1994-1996. A wannan lokacin kuma finafinan ma ba su sami bunkasuwa da karbuwa ba kamar littattafai. Kuma duk sauran finafinan da na fito, fitowa ce ta musamman sau daya ko biyu ko uku. Ka ga kuwa in ban karbu ba, ba wani abin mamaki ba ne. Sannan a yanzu ne na fito a cikin finafinai guda uku masu karfi a jere duk a matsayin jarumi daga shekarar 2017 zuwa 2018. Bayan haka kuma mu na iya cewa komai da lokacinsa; ta yiwu yanzu ne lokacin da karbuwar ta zo, domin komai ya na jiran lokacinsa, kuma hange ya kawo nesa kusa ba sai dai idan Allah ya kawo ta.
Shin da ma can ka fi sha’awar zama jarumin finafinai fiye da komai ne?
A a, ni ba jarumi na ke son in zama ba, marubuci na ke so in zama kuma na zama, na kuma kai kololuwa a zamanina kuma a fagena, domin in dai duniyar rubutun Hausa ce Ado Ahmad Gidan Dabino, MON, babu abin da zai cewa Allah sai godiya bisa wannan harka ta rubutu; Allah na gode ma ka.

Wasu na cewa kasancewarka marubuci ne ya sa ka ke iya isar da sakon da a ka dora ka a kai a cikin finafinai yadda ya kamata. Shin me za ka ce kan hakan?
Ba mamaki hakan ne, domin marubuci shi ya ke yin jarumi, shi ya ke mayar da shi sarki ko talaka, mai mulki ko marar mulki, attajiri ko matalauci, mutumin kirki ko na banza. Saboda haka idan har marubuci ne ya ke yin jarumi, idan a ka ba ni matsayin jarumi a matsayina na mai yin jarumi (marubuci) ashe faduwa ce ta zo daidai da zama. Na san abinda a ka ba ni in yi, kenan zan yi shi fiye da wanda bai san shi ba ko?

Mene ne bambancin zama jarumi da kasancewa marubuci?
Bambancin kamar na sama da kasa ne, tazarar ai yawa gare ta. Kowa ya na iya zama jarumi, amma ba kowa ne ya ke iya zama marubuci ba. Gaskiya ne, rubutu ya fi zama jarumi wahala sosai. Rubutu ya na bukatar yawan tunani da bincike. Dole, rubutu ya na bukatar ka iya karatu da rubutu. Jarumai kuwa akwai wadanda ba su iya karatu da rubutu ba, kuma sun yi shura a fagen jarumta.

A finafinan da ka fito, wanne ka fi so a ciki?
A yanzu dai wanda na fi so shi ne Juyin Sarauta, saboda wasu dalilai, kamar haka:
1. Shi ne ya sa na sami nomination na jarumin jarumai na Afrika (Zuma 2017)
2. Shi ne fim din da ya fara mayar da ni jarumin jarumai sau biyu a shekara daya (AMMA Award da 1st Kaduna International Film Festibal (2018).
3. Shi ne ya sa na zama fitaccen mai shiryawa (Best Producer, KILAF 2018).
4. Shi ne fim din da ya sami lashe kyautukan gasa (awards) guda 12, nomination guda 12 a cikin gida Nijeriya da waje, wanda a tarihin masana’antar Kannywood a shekara sama da ashirin da kafuwarta, shi ne fim daya (tilo) da ya taba samun irin wadannan kyautuka a cikin shekarar 2017 zuwa 2018. Kuma bai fito kasuwa ba, amma ya zama gagara gasa, cinye du (kamar yadda wasu a masana’antar su ke cewa).
5. Shi kuma fim din Kwana Casa’in yanzu a ka fara, ba a san irin rawar da zai taka ba tunda ba a gama ba. Fim din Bilkisu kuwa ba a gama editin ba, balle a kalle shi har a san ina ya dosa ko rawar da zai taka ba.

Lambar yabo nawa ka ci a matsayin jarumi?
Na sami lambar yabo guda biyu a matsayin jarumin jarumai a shekarar 2018 da kuma fitaccen mai shiryawa (Best Producer) duk a shekarar 2018.

Shin wane mataki ka ke son kai wa a matsayin jarumin fim?
Ina son na kai matakin jarumi mai finafinai marasa yawa, amma masu amfani ga jama’ata kuma duk fim din da na fito ciki na sami addua da fatan alheri sanadiyyarsa ko da bayan raina. Ba na so na zama jarumi mai taron yuyuyun finafinai marasa ma’ana da amfani ga jama’ata.

Exit mobile version