Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
Home SHARHI

Bambancin ‘Web Da Internet’

by Muhammad
February 21, 2021
in SHARHI
3 min read
Internet
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram

Daga Ibrahim Sabo,

(eltafseerpen@gmail.com)

samndaads

Mutane da dama suna  tunanin intanet da web ko yanar gizo ma’anarsu daya, saboda yadda ake amfani da su a wurare daban-daban ba tare da bambancewa ba, amma dai a zahirance suna da bambanci. Amma kafin mu yi magana a kan Web da Intanet din, zan dan yi bayani a kan ma’anonin kalmomin PAN, LAN, MAN da WAN atakaice.

Menene PAN?

Menene LAN?

Local Area Network shi ne LAN atakaice. Shi LAN sashin sadarwa ne da ya fi PAN karfi, wato za a iya yin dan nesa da na’urorin kuma su kasance suna hada juna. Misalan irin wadannan sashinan sadarwan sune wadanda ake yi a wata ma’aikata, ko wani gini, ko asibiti ko gida ko kamfani da makamantansu. Mutum zai iya hada na’urarsa a wannan sashen sadarwan matukar bai wuce kilomita guda tsakaninsa da magudanarwarta ba. Ana iya hada irin wannan sashin sadarwan a wurare da dama sannan a seta duk wasu lamura na gudanar da ita a wannan wuri ta yadda za ta kasance a wurin sai da mutane su zo su hada na’urorinsu da ita.

Menene MAN?

Metropolitan Area Network, shi ne MAN atakaice. Shi MAN ci gaba ne kuma babban LAN wanda ya kasance za a iya seta shi a babban birni ko wani yanki, wato za a iya hada wannan sashin sadarwan ko da mutum zai yi nisan kilomita 50 ko fiye da haka tsakaninsa da ita. Ke nan an samu ci gaba na sashin sadarwan LAN, ta yadda wannan sashin sadarwan yake iya hada na’urori dake gari daya ko wani yanki baki daya. Misalan irin wannan sashin sadarwan sun hada da gidan Rediyo ko ko Talabijin wadanda ake gudanar da su a gari daya, ko wani yanki.

Menene WAN?

Kamar yadda PAN ya kasance na mutum daya zuwa biyu, LAN ya kasance na wuri guda na ma’aikata, MAN ya kasance a birni ko kasa baki daya, haka nan shi kuma WAN ya kasance ci gabansu ne duka. Cikakkiyar kalmar WAN, shi ne ‘Wide Area Network’ dake nufin sashin sadarwa wanda zai mamaye kuma ya yi aiki a dukkanin nahiya ko kasa guda. Misalin irin wannan sashin sadarwan shi ne yanar gizo wato Intanet, wanda ita ma ta samo asali ne daga International Networking.

Menene bambamcin Internet da Web?

A duk lokacin da mutum ya bude na’urarsa ya shiga yanar gizo, hakan na nufin ya hada sashin sadarwarsa da miliyoyin sashinan sadarwa da ke wurare daban-daban a fadin duniya.

Amma abin da ake kira Web kuma shi ne shafukan da aka daura su a yanar gizo, misali jaridaralkuki.com.ng, Google.com, DailyTrust.com, leadershipayau.com da sauransu, dukkansu shafuka ne dake gudanar da aiyukansu a Intanet.

Kalmar Yanar Gizo

Fassarar kalmar yanar gizo kai tsaye zuwa turanci ita ce Intanet, domin ita ce hadakar da ta hada miliyoyin sashinan sadarwa daga mabambantan wurare a fadin duniya. Kalmar yanar gizo ta samo asali ne saboda fahimtar da da bahaushe ya yi wa intanet, cewa hadakar ce ta sashinan sadarwa, saboda ganin yadda gizo yake hada kowane lungu da sako na yanarsa. Duk da ma akwai bambamcin ra’ayi ga fassarar yanar gizo, ga masana harshen Hausa.

Amma Web kuma shafuka ne da aka daura su a wannan hadakar ta sashinan sadarwa, ta yadda mutum zai iya sada sashin sadarwarsa da wannan hadakar kuma ya iya shiga wani shafi don karanta abin da aka rubuta ta hanyar shiga adireshin shafukan da aka daura.

A shekarar 1969 aka kirkiri Intanet kuma tun daga wancan lokacin ya kasance sashin sadarwa mafi girma kuma mafi karfi.

Web kuma sai a shekarar 1989 aka samar da wannan fasaha ta daura shafuka a kan Intanet.

SendShareTweetShare
Previous Post

Gwamnatin Kano Ta Gargadi Masu Yi Wa Harkar Ilimi Zagan-Kasa

Next Post

Shekara Daya Da Fara Fitowa: Gudumawar Jaridar NATIONAL ECONOMY Ga Tattalun Azikin Nijeriya

RelatedPosts

NIS

Kwazon NIS Bisa Aiki Da Kundin Kula Da Iyakokin Kasa Na 2019-2023

by Muhammad
2 months ago
0

Daga Abdulrazak Yahuza Jere, Hukumar Kula da Shige da Fice...

Marigayi Sam

Al’ummomi Na Ci Gaba Da Bayyana Kyawawan Halayen Marigayi Sam Nda-Isaiah  

by Muhammad
2 months ago
0

Daga Idris Aliyu Daudawa,   Al’ummomi daban-daban na ci gaba...

Shin Wane Irin Tallafi Shirin ‘Future Assured’ Ya Yi A Kano?

Shin Wane Irin Tallafi Shirin ‘Future Assured’ Ya Yi A Kano?

by Sulaiman Ibrahim
2 months ago
0

A watan Mayu na wannan shekarar na rubuta Makala akan...

Next Post
National Economy

Shekara Daya Da Fara Fitowa: Gudumawar Jaridar NATIONAL ECONOMY Ga Tattalun Azikin Nijeriya

Domin sanya talla ko karin bayani a tuntube wannan numbar +2348126152609.

ADVERTISEMENT
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us

© 2020 Leadership Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2020 Leadership Group .

Go to mobile version