Abba Ibrahim Wada" />

Bamu Da Sa’a Akan Real Madrid – Neymar

Dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Paris Saint German, Neymar ya bayyana cewa ba su da sa’a ne kawai akan kungiyar Real Madrid, bayan da kungiyar ta su ta sha kashi da ci 3-1 a filin wasa na Santiago da ke kasar sipaniya.

Real Madrid ta yi nasara kan PSG ce a Gasar cin kofin zakarun Turai da suka kara a ranar Laraba a Santiago Bernabeu, wanda hakan ya sa Neymar ya ce akwai aiki a gabansu, wajen warware kwallayen da suka dauka a ragar su, idan an koma wasa na biyu.

PSG ce ta fara cin kwallo ta hannun Adrien Rabiot a minti na 33 da fara wasan, kuma daf da za a tafi hutun rabin lokaci ne Real Madrid ta farke ta hannun Cristiano Ronaldo a bugun daga kai sai mai tsaron gida wato fenariti.

Saura minti bakwai a tashi daga wasan Cristiano Ronaldo ya ci kwalo ta biyu, sannan Marcello Bieira Da Silba ya kara kwallo ta uku a raga.

Real Madrid da PSG sun taba karawa a gasar cin kofin Zakarun Turai a kakar 2015/16, inda suka tashi canjaras a Faransa a wasan farko a ranar 21 ga watan Oktoba, a wasa na biyu ranar 3 ga watan Nuwamba Real ta ci 1-0 a Spaniya.

PSG za ta karbi bakuncin Real Madrid a wasa na biyu a ranar 6 ga watan Maris din 2018 a kasar faransa inda suke bukatar su zura wa Real Madrid kwallaye biyu idan har suna son cigaba da kasancewa a gasar.

 

Exit mobile version