Abba Ibrahim Wada">
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
Home WASANNI

Ban Damu Da Karya Tarihin Pele Ba – Messi

by Abba Ibrahim Wada
January 5, 2021
in WASANNI
2 min read
messi
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram

Dan wasan gaba na kungiyar kwallon kafa ta Barcelona, Leonel Messi, ya bayyana cewa bai damu da karya tarihin tsohon dan wasan Barzil ba, Pele, duk da surutun da hakan ya janyo a kwanakin baya.

A kwanakin baya ne aka bayyana cewa dan wasa Messi ya karya tarihin da tsohin zakaran duniyar, Pele, ya kafa ta zura kwallaye masu yawa a kungiya daya, matakin da ya janyo cece-kuce game da adadin kwallayen.

samndaads

Ana cikin haka ne sai kungiyar Santos dake kasar Brazil, wato kungiyar da shahararren dan wasa Pele ya bugawa wasa a lokacin da yake matashi ta karyata zancen da akeyi na cewa dan wasa Lionel Messi ya karya tarihin dan wasa Pele wajen cin kwallaye a kungiya daya.

Messi, ya kamo tarihin da tsohon dan wasan Brazil, Pele, ya kafa na cin kwallaye 643 a kungiya daya, bayan kwallon da ya ci wa kungiyarsa ta Barcelona a wasan da ta buga da Balencia sannan ya sake zura kwallo daya wadda tasa ya zarta Pele din a wasan da suka fafata da Balladolid a satin daya gabata.

Santos ta ci gaba da cewa ana kokarin ragewa Pepe kwallaye 448 a cikin kwallayensa kuma a cikin kwallayen da ake son ragewa akwai kwallayen daya zura akan manya-manyan kungiyoyi a duniya ciki har da Inter Milan wadda take babbar kungiya a shekarar 1960.

Santos ta kara da cewa wasu daga cikin kungiyoyin da Pele ya zurawa kwallo a raga a lokacin da yake wasa akwai Riber Plate da Boca Juniors da Racing duka na kasar Argentina da Unibersidad de Chile da Real Madrid da Jubentus da Lazio da Napoli da Benfica da Anderlecht sannan sai ita kanta kungiyar da Messi yake bugawa wasa wato Barcelona inda a cikin wasanni hudu Pele ya zura musu kwallaye hudu.

Santos ta kara da cewa duka wasannin da Pele ya buga sun samu sahalewar hukumar kwallon kafa ta Brazil ko kuma ta yankin kudancin Amurka saboda haka wasannin da akace babu su a lissafi hukumomi ne suka amince ayi wasan saboda haka dole ne ayi lissafi dasu.

Messi ya buga wa Barcelona da ke Sifaniya wasanni a kakar wasa har 17 da ya yi, tun bayan fara wasansa a shekarar  2004 kuma gwarzon dan wasan Brazil ya fi kowa yawan cin kwallaye a kungiyar Santos a kakanni 19 da ya buga da kungiyar.

Har ila yau Messi na cikin manyan ‘yan wasan duniya da suke haskakawa sama da shekara 10 a jere, tare da takwaransa na Jubentus Cristiano Ronaldo wadanda cikin shekaru goma na baya suka mamaye kwallon kwafa ta hanyar lashe kowacce irin kyauta ta nuna bajinta.

Sai dai a wannan kakar Messi na fuskantar koma baya na rashin kokarin kungiyarsa ta Barcelona wadanda wasu ke dora alhakin hakan a kan shi duk da cewa a kwanakin baya ya bayyana cewa yana son barin kungiyar.

SendShareTweetShare
Previous Post

Har Yanzu An Kasa Samun Matsaya A Arsenal Kan Ozil

Next Post

Gwamnatin Tarayya Ta Kafa Gonakin Zamani Biyu A Jihar Edo

RelatedPosts

Alcantara

Alcantara Bai Dace Da Salon Wasan Liverpool Ba –Dietmar Hamann

by Abba Ibrahim Wada
12 hours ago
0

Tsohon dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Liverpool, Dietmar Hamann,...

Aguiro

Muna Bukatar Aguiro Ya Dawo Wasa – Guardiola

by Abba Ibrahim Wada
12 hours ago
0

Kociyan kungiyar kwallon kafa Pep Guardiola ya ce lallai Manchester...

Wenger Ozil

Wenger Ya Jinjina Wa Ozil

by Abba Ibrahim Wada
12 hours ago
0

Tsohon dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Arsenal, Arsene Wenger,...

Next Post
Gonakin Zamani

Gwamnatin Tarayya Ta Kafa Gonakin Zamani Biyu A Jihar Edo

Domin sanya talla ko karin bayani a tuntube wannan numbar +2348126152609.

Leadership Epaper
ADVERTISEMENT
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us

© 2020 Leadership Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2020 Leadership Group .

Go to mobile version