Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
Home LABARAI

Ban Damu Da Rashin Tabbatar Da Ni Ba –Ibrahim Magu

by Tayo Adelaja
August 9, 2017
in LABARAI
2 min read
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram

Daga Musa Muhammad, Abuja

Shugaban Hukumar EFCC, Ibrahim Magu ya bayyana cewa shi sam rashin tabbatar da shi a matsayin Shugaban Hukumar da majalisar dattawa ta ki yi bai dame shi ba, kuma ba zai taba damunsa ba, kuma kullum wannan abin da ke faruwa sai kara masa kaimi yake yi wajen ci gaba da bayar da tasa gudumawar wajen kawo karshen cin hanci da rashawa da sace dukiyar jama’a da ake yi a kasar nan.

samndaads

Malam Ibrahim Magu ya furta wadannan kalamai ne a cikin jawabinsa a wata ziyara ta musamman  da ya kawo babban ofishin LEADERSHIP da ke Abuja jiya Talata, wanda Shugaban kamfanin, Sam Nda-Isaiah tare da sauran manyan kamfanin suka tarbe shi.

Shugaban na EFCC ya ci gaba da cewa shi dama yaki da miyagun halaye abubuwa ne da dole sai an bi su a hankali, domin su masu aikatawa ba za su bari abubuwa su tafi a cikin dadi ba. Ya ce duk wadannan abubyuwa da suke faruwa tsakaninsa da majalisar, sakamakon yaki ne da rashawar, domin haka shi abin ma kara masa kaimi yake yi a akan abin da ya sa a gaba, tun ya samu gwamnatin da daukar wa kanta kawar da wannan mummunar dabi’a.

Cikin jawabinsa na maraba, Sam Nda-Isaiah ya nuna matukar farin cikinsa da wannan ziyara, wanda ya ce dama shi Magu ba bakon wannan kamfani ba ne, don haka ne ma kamfanin ya ba shi lambar yabo bisa kokarinsa wajen yaki da cin hanci da rashawa.

 

SendShareTweetShare
Previous Post

Shugaba Buhari Bai Karya Dokar Kasa Ba, Cewar Majalisar Dattawa

Next Post

Ziyarar Musamman da Shugaban Hukumar yaki da yi wa tattalin arzikin Nijeriya ta’annati (EFCC), Ibrahim Magu, ya kawo babban ofishin LEADERSHIP da ke Abuja jiya Talata, wanda Shugaban kamfanin, Sam Nda-Isaiah tare da sauran manyan ma’aikatan kamfanin suka tarbe shi.

RelatedPosts

Matar Al-Zakzaky Ta Kamu Da Cutar Korona, Inji Danta

Matar Al-Zakzaky Ta Kamu Da Cutar Korona, Inji Danta

by Muhammad
4 mins ago
0

Daga Khalid Idris Doya, Matar jagoran ‘yan uwa Musulmi a...

Zaben Dan Majalisa

Za A yi Zaɓen Gwamnan Anambara Ranar 6 Ga Nuwamba – INEC

by Sulaiman Ibrahim
5 hours ago
0

HUKUMAR Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta bayyana cewa a ranar...

Ogun

Fashewar Tankar Mai Ya Ci Rayuwar Mutum Uku Da Jittaka Shida A Ogun

by Muhammad
12 hours ago
0

Daga Khalid Idris Doya, A ranar Talata ne mutum uku...

Next Post

Ziyarar Musamman da Shugaban Hukumar yaki da yi wa tattalin arzikin Nijeriya ta'annati (EFCC), Ibrahim Magu, ya kawo babban ofishin LEADERSHIP da ke Abuja jiya Talata, wanda Shugaban kamfanin, Sam Nda-Isaiah tare da sauran manyan ma’aikatan kamfanin suka tarbe shi.

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Domin sanya talla ko karin bayani a tuntube wannan numbar +2348126152609.

Leadership Epaper
ADVERTISEMENT
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us

© 2020 Leadership Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2020 Leadership Group .

Go to mobile version