Connect with us

WASANNI

Ban Hana A Sake Siyo Ronaldo Ba, Cewar Mourinho

Published

on

Mai koyar da ‘yan wasan kungiyar kwallon kafa ta Manchester United Jose Mourinho ya bayyana cewa bai hana kungiyar ta sake siyo dan wasa Crostiano Ronaldo ba kamar yadda rahotanni suka bayyana.
A karshe satin daya gabata ne dai rahotanni daga kasar Ingila suka bayyana cewa kungiyar ta Manchester United taso ta sake siyo Ronaldo amma Mourinho yace bayason a sake siyo dan wasan.
Sai dai Mourinho ya karyata maganar a ranar Litinin a wata hira da yayi da manema labarai inda yace maganar Ronaldo bata taba zuwa wajensa ba kuma baisan da maganar ba saboda haka babu ruwansa.
“Maganar Ronaldo karyace kawai taku da ‘yan jarida amma bansan da maganar ba domin maganar sake siyo Ronaldo bata taba zuwa ofishi naba balle har ince wani abu akai” in ji Mourinho
Yaci gaba da cewa “Yanzu ba maganar siyo dan wasa bane a gabana tunda an rufe kasuwa abinda ayke akwai kawai shine yadda zamu cigaba da samun nasara a wasanninmu saboda mun fara kakar wannan shekarar da rashin nasara”
Manchester United dai ta farfado a wasan data buga da kungiyar Burnley a gasar firimiya bayan tayi rashin nasara a wasanni biyun data buga a baya wanda hakan yasa aka fara maganar cewa kungiyar zata koreshi.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: